WASU MATAN SU KE 'DAUKAN 'DAWAINIYAR GIDAJEN SU !!! - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, January 7, 2019

WASU MATAN SU KE 'DAUKAN 'DAWAINIYAR GIDAJEN SU !!!

WASU MATAN SU KE 'DAUKAN 'DAWAINIYAR GIDAJEN SU !!!
.
Haqiqa wasu Matan suna cikin matsanancin halin rayuwa musamman yanda mazajensu suka sake musu komai kama daga kan ciyarwa, Tufatarwa, kud'in makarantar yara, kud'in haya, duk wani d'awainiyar dake kan namiji sai ya sakewa matarsa.
.
Idan wasu matan suna labarta maka irin wahalhalun da suke ciki ko kuma ka gani da idonka haqiqa zaka tausaya musu. Wannan wani irin rashin imani ne ka rabo mace da iyayenta da 'Yan uwanta da danginta tare da amincewa da Sharad'in da musulunci ya jingina ga Haqqin aure, ai koda tana aikin Gomnati bai dace ka sake mata dukkan d'awainiya ba, bal ma wasu matan ba aikin da suke yi amma a hakan ake sake musu d'awainiyar gidajensu.
.
Koda dai wata matsala aka samu bai dace ka sake mata komai akanta ba, domin ita mace Idan ta soka har ta amince kukayi aure tana sonka ne da dukkan zuciyar ta, amma hakan bai hana tayi maka laifi, duk lokacin da mace tayi maka laifi to ka tuna soyayyarta da tama, ka tausayawa raunin ta, kayi mata afwa, ka mu'amalance ta kyakkyawar mu'amala tare da tausasa lafazi da kyautata aiki a gare ta da bata dukkan haqqoqinta.
.
ALLAH (SWT) yana cewa: (kuyi musu mu'amala da kayautatawa in kunqi su (saboda wani abu da sukayi) ya fusata ku kin wani abu kuma ALLAH ya sanya alkhairi mai yawa a cikin sa)
.
[Suratul Nisa'i: 19]
.
Koda yake Matan suna kasancewa cikin wannan yanayin ta hanyoyi da dama daga ciki:
.
◉Wata matar ta auri lalataccen miji jahili a addini da rayuwa, maras lissafi da tunani, wanda bai san darajar mace ba balle yasan darajar 'Ya'yan da ya haifa, Ya d'auki aure kawai a matsayin yaji dad'i da mace kawai shine aure awajensa, idan iya shegensa ya motsa haka zaizo ya jibgeta kamar Wanda ya samu jaka akan laifin da bai taka kara ya Karya ba, bai damu da damuwarsu da yadda suka rayu ba ya suke ci, ya suke sha ba, irin wannan lalataccen mijin bayi da kunya haka zaije ya dawo d'an abunda suka kalata don cikinsu haka zaizo ya bud'e dargajejen bakinsa ya d'ura. ALLAH kada ka jarabce mu da irin wad'annan mazajen (Ameen)
.
◉Wata matar kuma larura ne ya samu mijin kodai ta rashin lafiya (jinya) ko kuma na karyewar arziki da rashin samun mafakar inda zai ringa samun abunda zai ciyar dasu, wannan dalilin yana iya zamowa mace ta d'auki d'awainiyar gidanta don ganin qoqarin dai sun rayu cikin walwala, ga yanayin rayuwar da ake ciki anan nigeria kana son taimakawa d'an uwanka ma kaima baka dashi.
.
◉Wata Matar kuma Mijin Ya mutu ya barta da 'Ya'ya, ko kuma boko haram sun kashe mijin ko kuma sun tarwatsa musu rayuwa, babu yadda matar ta iya haka zata d'auki d'awainiyar kula da 'ya'yanta da kanta, ga rayuwar yadda ta zama kowa yana fama da kanshi.
.
◉Wata matar kuma mijin yana da yadda zai yi ya ciyar dasu kuma ya tufatar dasu ya kuma d'auke musu dukkan d'awainiyar su, to amma Rashin tsoron ALLAH ke sanya shi tauye musu haqqinsu yayi watsi da dukkan damuwar su, a hakan kuma bayan ya tauye haqqoqin iyalansa sai kaga yana qoqarin qaro wani auren ko kuma ka samu yana bin matan banza yana sake musu kud'i alhali bai biya haqqin wacce ya ajiye da sunan auren Sunnah ba balle kuma 'Ya'yan data haifa. ALLAH kada ka Jarrabemu da irin wad'annan Mazajen, Ya ALLAH ka shirye su (Ameen)
.
Mazaje kuji tsoron ALLAH, Ya kamata ku ringa tausayawa iyalanku ku daina tauye musu haqqoqin su, ku ciyar dasu ku tufatar dasu ku kyautata musu ku mu'amalance su da kyakykyawar d'abi'a. Hakanan wad'anda suka rasa mazajensu a tausaya musu acikin al'umma, duk da kasancewar wannan lokaci da muke ciki lokaci ne wanda mafi yawan mutane kowa yana garuwa, amma a hakan za'a tausayawa juna ko don albarkacin wannan wata mai alfarma da muka fuskanta.
.
Ya ALLAH dukkan Mazajen da ke sauqe Haqqoqin Iyalansu ALLAH ka qara wadata su, Wad'anda kuma basa iya sauqe haqqoqin iyalansu ALLAH ka basu iko da damar sauqewa, Wad'anda kuma suke da dama amma saboda rashin tsoronka suke tauye haqqoqin iyalansu Ya ALLAH ka shirye su, Masu taimakon Al'umma ta hanyar ciyarwa da tufatarwa da ilimantarwa ALLAH Ya saka musu da mafificin alkhayri (Ameen)
.
#Repost.
#FaridahBintuSalis.
#Bintusunnah.

No comments:

Post a Comment