SHIRU HIKIMA CE !!!
.
SHIRU: Yana daga cikin mafi girman ladabin da ya wajaba ma'abota hankali su lizimta. A koda yaushe Shiru mai ma'ana yafi surutu maras ma'ana. Ana yin da-na-sani ne akan magana, amma ba a cika yi akan kawaici ba.
.
→Wani mai hikima yake cewa: “idan har kayi nadaman shiru sau daya, Toh kuwa zakayi nadamar magana sau da yawa. Don haka ka kama bakinka duk lokacin da baka tabbatar da amfanin magana ba.
.
Shiru ado ne mai kyalkyali ga ma'abotansa, har'abada Yawan surutu ko gatari ne mai sassake ma mutum mutuncinsa ta barshi tsirara. Wani lokaci Shiru shine yaren da zuciya tafi fahimta Samada kalmomin da baki yakan sarrafa sautukansa.
.
Yana da kyau mutum yasan cewa ba dukkan abunda aka sani ake fada ba. Haka kuma ba kowace magana ce ake bada amsarta ba, ko shiru ma magana ce !!!
.
Shiru hikima ce ba wauta bace kuma ba rauni bane face dai sanin abunda ya dace ne, kuma ba kowa ne yake iya kame bakinsa yayi shiru ba, Amma kuma duk lokacin da aka shimfida tabarmar shiru, to hankali da hikima ne zasu zauna akai.
.
Kada kayi tsammanin cewa; duk wanda ya yi shiru kurma ne. Wani ya yi shiru ne yana jiran lokaci. Wani ya yi shiru ne don yana nazari. Wani kuma kawaicinsa shi ne maganarsa.
.
Ba abin burgewa ba ne mutum ya zamo mai yawan surutu, ka yawaita shiru kada ka ce komai sai da buqata.
.
→ Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Idan kayi imani da ALLAH da ranar karshe Toh ka fadi alkhairi ko kayi shiru.” [Al-hadith]
.
→An tambayi wani ma'abocin Hikima: a ina ka koyo Hikimarka? Sai yace: A wurin wawaye da jahilai, Kamar yaya? Yace: idan suka yi maganar wauta ko jahilci sai inyi shiru, sai hakan ya karamin hikima.
.
→ Imam az-zahaby (Rahimahullah) Yace: "Idan fitina ta auku to kayi riqo da sunnah, ka lizimci shiru, kada ka ringa Kutsawa acikin abinda bai shafeka ba, duk abinda ya cukuikuye maka ka mayar dashi izuwa ga ALLAH da Manzonsa ka tsaya kace ALLAH ne masani " [Siyaru 20/141]
.
→ Wani sashen ma'abota hikima suna cewa: “Ka lazimci shiru domin shi zai baka kyakkyawar soyayya, kuma zai amintar da kai daga muguwar mamaya, sannan zai sanya maka tufafin nutsuwa, sannan zai ishe ka kyakkyawan guzuri.” [Aadabud-Dunya Wad-Deen: 290-292]
.
Amma duk da wadannan takaitattun bayanan da suke nuna fifikon yin shiru fiye da yin magana, hakan bazai sa ayi Shiru yayin da aka ga cutarwa ga wani ko al'umma ko kuwa addinin ALLAH ba. Wannan asali ma wajibi ne Ayi iya kokari wajen kawar da zalunci da azzalumai amma mutum yayi magana akan abunda ya sani yaja bakin shi yayi shiru akan abunda bai sani ba hakan shine mafi alkhairi.
.
#Repost.
#FaridahBintuSalis.
#Bintussunnah.
Monday, February 18, 2019
New
SHIRU HIKIMA CE !!!
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
FAGEN ADDINI
Tags
FAGEN ADDINI
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment