[[JAMB 2019]] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, March 12, 2019

[[JAMB 2019]] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB?

Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 

Kashi Na 4

( 08-03-2019)

•Shin Ban iya Computer Bane? 

•Shin Ban iya Karatun Bane? 

•Mecece Matsalar? 

Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka. 

Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
 Jarrabawar JAMB,

 Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba! 

a ina Matsalar Take? 

•>Matsala Ta Shida

•Rashin iya managing din time(Rashin iya lura da lokaci):-
A lokuta dayawa Dalibai sunayin karatu yanda yakamata, kuma abinda suka karanta yana fitowa a cikin wannan jarrabawa, amman saidai kash!!! lokaci yana samar musu da matsala, saboda basu da saurin da zasu iya kammala amsa tambayoyin nasu a lokacin da hukumar ta kayyade na awa 2.

Hakanne yasa suke rasa maki maiyawa, daga karshe kaga sun fadi wannan jarrabawa.

  To ammafa dalibai kada kutsorata, domin bawai lokacin ne yakeyin kadan ba, awa 2 zata isheka/isheki kugama amsa tambayoyinku guda 180 harma kayi ragowa, matukar zakabi lokacin naka yadda yakamata, ma'ana basai kayi saurin daya wuce kimaba kuma karka tsaya wasa(lala) har lokacin naka yakare.
Mafita akan wannan matsalar:-
 1- Dalibi yatabbatar dacewa ya amsa tambayoyinsa cikin sassarfa ma'ana basauri sosaiba kuma ba lalaba.

2- Dalibi yatabbatar dacewa yana lura da lokacinsa alokacin dayake amsa jarrabawar. 
3- Dazarar dalibi yaga cewa lokacinsa yarage kadan misali seconds 20, to yayi submitting duk da cewa jamb ta tsara abin akan cewa lokacinka yana cika computer zata dauke tayi submitting dakanta to amma wasu lokutan akan iya samun matsala.

•>Matsala Ta Bakwai

•Rashin yin addu'a:-

Duk da dai nasan cewa dalibai dayawa zasuce meya kawo wannan a cikin dalilan faduwa jamb?to kuwa akwai dalili:-

Domin babu addinin da bai yarda da addu'aba,either musulinci ko kiristanci. 

Hakika Jarrabawa mai hadari irin jamb tana bukatar addu'a fiyeda kowacce jarrabawa. 

Kuma addu'ar bawai taka kai kadaiba, A'a wannan addu'ar ta hada da addu'ar iyaye,yayyu,kannu dadai sauran dangi, saboda addu'arka kai kadai aganina bazata wadatarba dole sai an hada data walidai.

•Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-

1•Dalibi yatabbatar dacewa yayi addu'a kafin dakuma bayan yin jarrabawarsa

2•Sannan yatabbatar addu'ar iyayensa tashigo ciki, domin addu'arsu karbabbiyace, musammanma ta uwa 

3• Sannan da addu'ar kannai,yayyu dadai sauran dangi baki daya

4•Ina ganinma idan Allah yahorewa dalibi yadingayin sadaka, tareda sanar da masallatan unguwarsu cewa a tayashi da addu'a akan wannan bukata tasa.

By:- Miftahu Ahmad Panda (Special Assistant to Secretary General of Asof).

DAGA TASKAR ASOF.

Zamuci Gaba insha Allah. Ta hannun arewagist.com.ng

1 comment:

  1. Hello my fellow student, my name is Martha i would like to use this medium to thank mr wale who helped me upgrade my waec result, i had written many times but could not make me maths until i got Mr. WALE number from a friend i called him my problem, i was shocked when the next day he sent me a pin, which i used in checking my result, and if God would have it i made my maths b3, friends i was also told that he help in the upgrade of all kind of result, he even helped my sister with her 2010/12 result which were want hero. You can call him now on +2347058236867 or 07058236867 if you need your waec result if you need your jamb result if you want to upgrade your jamb you want to upgrade results If you lost your result If you have not seen your result If you need answer for any exam Now you need to pass school or level result for your working place call now +2347058236867 or 07058236867

    ReplyDelete