Masu fashin bakin siyasa a Najeriya na nuna shakku dangane da yiwuwar dinke barakar da ta kunno kai a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya duk da sabon kwamiti da aka kafa domin warware matsalar da ta dabaibaye jam'iyyar.
Masana kimiyyar siyasa a Najeriya, irin su Farfesa Jibrin Ibrahim na da ra'ayin cewa "samar da sulhu a jam'iyyar APC abu ne mai wuya kasancewar an riga an ja daga tsakanin bangarori guda biyu."
Ya kara da cewa babban kalubale da ke gaban wannan kwamiti shi ne " lokacin da za a dauka kafin ma a zauna da bangarorin da ba sa jituwa da juna."
Ya kuma kara da cewa duk da an kafa kwamitin samar da zaman lafiya " idan bangare daya ya fahimci cewa kwamitin ya karkata ga daya bangaren to ba za a taba samun jituwa ba, domin haka rikicin da aka dade ana yi a jam'iyyar ba lallai ba ne a samu mafita ba."
Farfesa Jibrin Ibrahim ya kuma ce "kamar yadda kojwa ya riga ya sani wannan jam'iyya ta rabu gida biyu, inda tsagin farko ke son duk juyin da za a yi a bai wa Bola Ahmed Tinubu takara a zaben 2023, inda shi ma daya bangaren na da nasa dan takarar."
Ya kuma ce sabanin yadda ake tafiyar da tsarin siyasa a duniya, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce " a Najeriya dukkan bangarori masu rikici suna son suyi galaba ne a saboda haka babu yadda za a yi a samar da sulhu.
Yayin wani zaman gaggawa ranar Alhamis wanda shugaba Buhari ya halarta, Majalisar koli ta jam`iyyar APC ta kafa wani kwamitin mutum 13 da zai bi hanyoyin sulhunta `ya`yan jam`iyyar, tare da magance rikicin da ya dabaibaye ta, wanda ya yi sanadin raba kan `yan kwamitin gudanarwar jam`iyyar da aka rusa.
Shugaban kwamitin wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya ce zai aiki da dukkannin bangarorin sannan kuma zai tabbatar da an yi adalci.
To sai dai 'yan sa'o'i bayan nan ne kwamitin gudanarwar da aka rusa, ya ce zai garzaya kotu domin neman kuliya ya bi masa hakkinsa bisa zargin rashin halascin rushe shi da akayi.
Wata sanarwa da aka aike wa kafafen yada labarai mai dauke da sa-hannun Hilliard Etta wanda yake ikrarin shi ne shugaban jam'iyyar APC na kasa na rikon kwarya da Waziri Bulama da ke ikrarin kasancewarsa sakataren watsa labarai na jam'iyyar da kuma karin mambobi 15, tsohon kwamaitin gudanarwar ya bayyana " taron majalisar zartarwar APC da aka yi da haramtacce wanda kuma ya yi tsarin mulkin jam'iyyar karan tsaye."
Sanarwar ta kara da cewa " Victor Giadom ba shi da hurumin kiran taron gaggawa na Majalisar Zartarwa."
A ranar Laraba ne dai Shugaba Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam'iyyar APC na kasar.
No comments:
Post a Comment