wanda a yanzu shine zai tsaya takarar Gwamna a PDP
Gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki ya lashe zaben fiddan gwanin dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.
Jam'iyyar ta bayyana hakan da yammacin Alhamis bayan kammala zaben a babban filin kwallon Samuel Ogbemudia, Benin City, babbar birnin jihar Edo.
A filin zaben da ya gudana ranar laraba, an samu halartar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da sauran manyan jam'ian jam'iyyar.
Hadimin gwamna Obaseki kan Soshiyal Midiya, Jack Obinyan, ya bayyana hakan a shainfa na Tuwita.
Yace: " Ko da baka samu labari ba, gwamna Obaseki ya lashe zaben ba tare da fuskantar wani kalubale ba, shi kadai ne dan takarar PDP."
"Za'a gudanar da zaben ranar 19 ga Satumba, 2020."
Godwin Obaseki ya samu wannan nasara ne bayan dukkan abokan takararsa sun janye masa duk da cewa shi ne na karshen da aka tantance cikinsu.
Da farko, Gideon Ikhine, ne ya fara janyesa masa, sannan Omoregie Ogbeide-Ihama wanda ya shiga kotu a baya domin a hana Obaseki takara amma ya janye daga karshe.
Na karshe shine Kenneth Imasuagbon wanda ya janye da safiyar ranar laraba a filin zabe.
Yanzu za'a kara tsakanin Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP da Osaze Ize-Iyamu na jam'iyyar APC. Wadannan yan takara biyune suka goge raini a shekarar 2016 kuma zasu sake yanzu.
Babban ci shine kawai sun sauya jam'iyya.
No comments:
Post a Comment