Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin ci gaban Afrika AfDB, Adesina - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, June 2, 2020

Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin ci gaban Afrika AfDB, Adesina


Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin  ci gaban Afrika AfDB, Adesina

A yanzu dinnan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan labule tare da shugaban bankin Afrika, Dr Akinwumi Adesina, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin Mista Adesina tare da shugaban ma'aikatan fadar shugabna kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, inda suka shiga ganawar sirri gadan-gadan.

Sauran manyan jami'an gwamntin tarayya da suka gana da Mista Adesina tare da shugaba Buhari sun hadar da Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed.
Sai kuma Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina da sauransu.

AfDB, cibiyar hadin gwiwa ce mallakin kasashen Afirka wadda kasar Amurka ta kasance babbar mai hannun jari a cikinta.

Shugaba Buhari da sauran shugabannin Afirka, na ci gaba da nuna goyon baya a kan Adesina, wanda zai cika wa’adinsa kuma yana da damar a sabunta shi na wani tsawon shekaru biyar.

A baya-bayan nan ne aka hurawa Mista Adesina wuta akan zargin nuna bangaranci da wariya wajen nade-naden manyan mukamai a bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB).

Sai dai hukumar gudanarwa ta bankin ta wanke Adesina da zargin da ake masa, lamarin da tace ba za ta nemi ya sauka daga mukaminsa ba.

Mai magana da yawun bankin, Niale Kaba, ta ce babu wata matsalar shugabanci ko ta tsarin mulki a bankin.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa.

No comments:

Post a Comment