Janar Burutai ya gana da shugaba Buhari kan yakin Boko Haram
- Babban hafsan sojin ya koma jihar Borno da zama har sai an kawar da yan Boko Haram
- Ya ce dakarun Sojin suna samun gagaruman nasarori kan yan ta'addan kuma ba zasu yi kasa a gwuiwa ba.
Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Burutai, ya bayyana cewa dakarun sojin dake Arewa maso gabas sun hallaka yan Boko Haram 1,429 cikin watanni biyun da suka gabata.
Jami'an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga- Gudaji Kazaure https://youtu.be/EVauMKSVUq4
Haka zalika an damke masu kaiwa yan ta'addan rahotannin leken asiri 166.
Buratai ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari yau Litinin 8 ga watan Yuni, 2020 inda ya ce ana samun gagarumin nasara wajen kawar da yan ta'addan.
Babban hasfan Sojin ya bayyana cewa yana kyautata zaton za a cigaba da samin cigaba wajen yaki da yan ta'addan.
Jami'an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga -ho. Gudaji Kazaure
Yace: "Dakarun Sojin na iyakan kokarinsu kuma hakan na haifar 'da mai ido saboda irin nasarorin da muke samu."
"Har yanzu ana gabza yaki kuma an hallaka sama da yan Boko Haram 1,429 kuma mun damke yan leken asiri, jagorori, masu kai musu kaya 166 a cikin kauyuka da dazuka."
"Saboda haka, wannan babban nasara ne, jami'an leken asirinmu tare da jami'an DSS da kuma abokanmu na kwarai yan sa kai CJTF, sun nuna bajinta domin ganin an samu wannan nasaran."
Majalisa ta nemi a Kara daukar sojoji dubu Dari 100,000
"Ina tabbatar muku da cewa abubuwa za su cigaba da kyau cikin yan kwanakinnan."
Buratai ya ce hukumar bata mayar da hankalinta Arewa maso gabas ba kadai, har da sauran sassan kasar dake fuskantar barazanan tsaro.
Yace: "Zamu cigaba da kawar da yan ta da zaune tsaye, ba a Arewa maso gabas ba kadai, dama dukkan sassan kasa."

No comments:
Post a Comment