Gwamnoni Arewacin Najeriya sun amince da yin amfani da ‘yan banga da maharba wajen yaki da 'yan bindiga da duk wani nau'in rashin tsaro da ke yankin da zakulo bayanan sirri da za ayi amfani dasu wajen kawo karshen kashe-kashe a yankin.
A taron da kungiyar gwamnonin ta gudanar a kafar internet ta hanyar Teleconferencing, sun nuna alhilinsu kan kashe-kashen dake ta faruwa a yankunan Katsina da Zamfara da Sokoto da sauran wuraren.
Sanarwar bayan taron ta bayyana cewar matsayar da gwamnonin suka dauka sun hada da: ” Nada tsayayyen kwamitin tsaro a Arewa da zai yi aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da matakan tsaro a yankin.
“Gwamna Yahaya Bello ne na Kogi zai jagoranci gwamitin, sai kuma gwamnonin Zamfara da Gombe a matsayin mambobi”.
Gwamnonin sun Sami jagorancin gwamna Simon Lalong na Filato, sai kuma gwamnonin Sokoto da Adamawa da Neja, a matsayin mambobi.
Kwamitin zai kuma tuntubi sarakuna da malaman addini da kuma shugabbanin al’umma domin ganin an fadada hanyoyin tabbatar da ganin an dakile matsalolin tsaro a yankin.
“Za su yi amfani da ‘yan banga da maharba da masu sa ido a cikin al’umma da kungiyoyin da Kai a tsarin tsaro na yankin domin zakulo bayanan sirri da za a yi amfani dasu wajen dakile rashin tsaro.”
Gwamnonin sun tausaya wa wadanda bala’in ya auka wa da kuma ba su kwarin gwiwar cewa gwamnatocin jihohi da ta tarayya na bakin kokarin ganin an shawo kan rashin tsaro da kuma magance matsaloli na yau da kullum da fitintunun da suka janyo wa wadanda abin ya shafa.
Daga karshe suka roki jami’an tsaro da su mayar da hankali wajen ganin sun kawo karshen kashe-kashe ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a kasar.
No comments:
Post a Comment