Kotu ta mayar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano 5 da aka dakatar
Wata babbar Kotun tarayya dake zamanta a jihar Kano ta warware hukuncin majalisar dokokin jihar Kano na dakatar da wasu mambobinta biyar.
An dakatar da mambobin ne sakamakon kaurewar rikici a zauren majalisar, inda suka Nuna adawa yayin da aka gabatar da kudirin neman tsige tohon sarki Sanusi II
- Alkalin kotun, Jastis Lewis Alagoa, ya ce da katar da 'yan majalisar ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.
kotun ta soke hukuncin dakatar da mambobin majalisar dokokin jihar Kano 5 da ka kakin majalisar Abdul Aziz Garba gafasa yayi saboda sun nuna adawa da tsige tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
A ranar 15 ga watan Maris ne majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da mambobinta guda biyar bisa zarginsu da hannu a sace sandar ikon majalisa yayin sauraren kudirin neman bincike da tsige Sanusi II.
'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da; Ya'u Gwarmai mai wakiltar mazabar Kunci da Tsanyawa, Labaran Abdul Madari mai wakiltar mazabar Warawa, Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa.
Ragowar sune; Mohammed Bello mai wakiltar mazabar Rimingado da Tofa, da Salisu Ahmed Gwangwazo mai wakiltar mazabar birnin Kano.
Da ya ke zartar da hukunci a ranar Laraba, alkalin kotun, Jastis Lewis Alagoa, ya ce dakatar da 'yan majalisar ya sabawa kundin tsarin mulki.
Alkalin kotun ya bukaci majalisar ta gaggauta janye dakatarwar tare da biyan 'yan majalisar dukkan albashi da alawus dinsu na tsawon lokacin da aka dakatar da su.
A ranar 16 ga watan Maris ne aka tsige Sanusi II bisa zarginsa da almudahana dukda an samu hargitsi a majalisar dokokin jihar Kano bayan 'yan majalisar biyar sun hada kai tare da kalubalantar kudirin neman a tsige tsohon sarkin.

No comments:
Post a Comment