Majalisa ta gayyaci Kamfanin Julius Berger kan Rashin Saurin aikin titin Abuja zuwa kano - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, June 28, 2020

Majalisa ta gayyaci Kamfanin Julius Berger kan Rashin Saurin aikin titin Abuja zuwa kano

Majalisar Wakilan Najeriya ta gayyaci kamfanin Julius Berger da ke aikin titin Abuja zuwa Kano ya gurfana a gabanta saboda rashin saurin aikin duk da cewar an samar da isassun kudin yin sa.

Kaza lika Majalisar na neman bayanai daga kamfanin kan tafiyar hawainiyar aikin titin Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Neja ta biyu.

Wakilin Aminiya ya ji daga majiya kwakkwara a Majalisar na cewa jami’an Julius Berger za su bayyana a gaban Kwamitin Majalisar na Ayyuka a ranar 7 ga watan Yuli, sai dai majiyar batayi karin haske ba.

Sama da shekara biyu ke nan kamfanin ke aiwatar da manyan ayyukan, sai dai korafe-korafe sun yawaita kan rashin kammala su.

Tun a watan Fabrairu Majalisar ta fara binciken tafiyar hawainiyar ayyukan duk da cewa an biya isassun kudin aiwatar dasu.

Karo na biyu ke nan da kamfanin zai bayyana a gaban kwamitin kan rashin saurin aikin.

A watan Disamban 2019 ma majalisar ta gayyaci kamfanin kan wannan matsalar wanda a wancan lokacin gayyatar da hada da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya da kuma Hukumar Kare Aukuwar Hadurra ta Kasa (FRSC).

No comments:

Post a Comment