Rundunar 'yan sanda ta yi HOLEN dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi holen wasu manyan masu laifi a hedikwatarta ta kasa dake birnin tarayya, Abuja.
Daga cikin masu laifin da rundunar 'yan sanda tayi holen, akwai dilolin makamai, 'yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane.
An yi holen masu laifin tare da mugayen makaman da aka kama a wurinsu.
A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa cewa rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kubutar da wasu leburori fiye da 600 da aka tursasawa zama a cikin wani kamfanin sarrafa shinkafa mai suna 'popular farm rice' dake rukunin masana'antu na Challawa a Kano.
Ma'aikatan da abin ya shafa sun shaidawa jaridar Premium Times cewa an yi musu barazanar sallama daga aiki ga duk wanda ya yi kokarin barin kamfanin domin zuwa ya gana da iyalinsa.
Jami'an rundunar 'yan sanda sun dira a kamfanin bayan samun sahalewar kotu, sun sallami ma'aikatan tare da kama manajojin kamfanin guda hudu.
A cewar ma'aikatan, an hanasu barin harabar kamfanin ne saboda tsoron kar su kwaso cutar korona daga waje idan sun fita.
Daya daga cikin ma'aikatan da aka kubutar ya shaidawa manema labarai cewa bai kara fita daga kamfanin ba tun bayan shigarsa a ranar 23 ga watan Maris.
Haruna Salihu, wani ma'aikacin kamfanin ya ce ba'a bar shi ya fita daga kamfanin ba tun bayan shigowarsa a ranar 28 ga watan Maris.
No comments:
Post a Comment