Facebook zai Samar da Internet Mai Arha a Africa - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, July 23, 2020

Facebook zai Samar da Internet Mai Arha a Africa

Kamfanin sada zumunta na Facebook ya bayyana cewa hannun jarin da ya zuba kan intanet zai jawo wa nahiyar haɓakar tattalin arziƙi da kusan dala biliyan 60 zuwa 2024.

A wani rahoto da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa ƙaruwar mutane a shiga intanet zai sa kuɗin intanet ɗin ya ragu a nahiyar.

Kamfanin na Facebook ya ce yana zuba kuɗi wurin samar da kayayyakin haɓaka intanet ɗin wanda hakan zai bada dama ga mutane masu zama a kudu da hamadar sahara su samun intanet cikin sauƙi.

A halin yanzu, kamfani na Facebook ya samar da wi-fi ta intanet a ƙasashe bakwai ga kusan mutum miliyan huɗu a Uganda da Najeriya.

Sama da rabin mutanen da ke kudu da hamadar sahara ba su da damar shiga intanet, kuma intanet É—in na da tsada idan aka haÉ—a da sauran nahiyoyi.

Magu ya ƙalubalanci Malami ya kawo shaida guda daya tal inda ya karbi toshiyar baki
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/magu-ya-alubalanci-malami-ya-kawo.html

No comments:

Post a Comment