Gwamna Ganduje Zai Jagoranci Kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, July 2, 2020

Gwamna Ganduje Zai Jagoranci Kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo

Gwamna Ganduje Zai Jagoranci Kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo

Kwamitin rikon kwarya na Jam'iyar APC Karkashin H.E Mai Mala Buni ya nada Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban tawagar Jam'iyar na kasa da zaiyi gangamin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo.

A ranar 19 ga watan Satumba mai zuwa ne za'ayi zaben Gwamnan Jihar ta Edo.

Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da mukaddashin sakataren Jam'iyar APC na kasa Yekini Nabena ya fitar, tawagar yakin neman zaben Gwamnan Jihar ta Edo zata kunshi karin Gwamnonin Jam'iyar masu ci guda 4 da mataimakin shugaban majalisar dattawa da tsoffin shhugabannin Jam'iyar 2.

Za ayi bikin Kaddamar da Kwamitin a ranar litinin 6 ga watan yuli insha Allah a shedikwatar Jamiyyar APC ta Abuja.



No comments:

Post a Comment