Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarki da Shugaban ƙaramar hukumar Misau - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Friday, July 3, 2020

Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarki da Shugaban ƙaramar hukumar Misau

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Kaura, ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Sulaiman sakamakon tashin hankali da aka samu a yankin tsakanin manoma da makiyaya.

An sami Tashin hankalin ne a wannan makon, a garin Zadawa da ke cikin karamar hukumar ta Misau, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutune tara da jikkata wasu da dama.

Gwamna Bala Kaura ya sanar da dakatar da Sarkin ne yayin kaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikici mai nasaba da wani fili da ake takaddama a kai.

Gwamnan na jihar Bauchi ya kuma dakatar da Shugaban ƙaramar hukumar Misau da wasu sarakunan gargajiya masu mukaman hakimi da dagaci a yankin da rikicin ya shafa.

Yayin taron, Gwamna Bala Muhammad ya rantsar da sabon shugaban rikon karamar hukumar Honorable Isah Kufai tare da kiransa da yayi aiki da kwamitin da aka kafa don lalubo musabbabin rikicin.

Sarkin Misau dai na daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar ta Bauchi.

Tun farko gwamnan ya dakatar da shugaban riko na karamar hukumar ta Misau da wasu manyan jami’an karamar hukumar. Gwamnatin jihar na zarginsu da yin sakaci game da rikicin.

Gwamnan ya ce an dakatar da jami’an da sarakunan gargajiyar ne domin bayar da damar gudanar da bincike. 

Dakatarwar za ta ci gaba da aiki zuwa lokacin da za a kammala bincike.

An ba kwamitin binciken da aka kaddamar makwanni uku ya gabatar da rahotonsa. 

Kawo yanzu ba a kai ga jin ta bakin shuwagabannin da aka dakatar ba.

Ba a dai cika samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Bauchi ba idan aka kwatanta da wasu jihohin Najeriya masu fama da irin wannan rikici da ma matsalar ‘yan bidiga.

No comments:

Post a Comment