Pantami ya taka wa hukumar NIPOST burki kan ƙara kuɗin rajista - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, July 26, 2020

Pantami ya taka wa hukumar NIPOST burki kan ƙara kuɗin rajista

Pantami ya taka wa hukumar NIPOST burki kan ƙara kuɗin rajista

Ministan ya ce sabon tsarin ba ya cikin dokokin da ya sahale wa hukumar ta aiwatar

Ministan Sadarwa a Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami ya yi watsi da sabon tsarin kuɗin neman lasisi ko rajista a kan kamfanonin kai saƙo da Hukumar Aika Saƙonni ta Najeriya (NIPOST) ta fito da shi.

Dr. Pantami ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wani saƙon Twitter da ya wallafa, yana mai cewa hukumar ba ta samu sahalewarsa ba domin aiwatar sabon tsarin.

"Mun samu labarin wani ƙari game da kuɗin rajista, wanda ba ya cikin dokokin da na sahale muku," in ji Pantami.

"An shaida wa shugabanku a jiya cewa su dakatar da shirin sannan su aiko da rahoto ga ma'aikatarmu zuwa ranar Litinin. Ina yi muku fatan alheri."

PDP ta buƙaci Buhari ya yi murabus saboda rashin tsaro
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/pdp-ta-buaci-buhari-ya-yi-murabus.html

Daga cikin sabon tsarin da Nigerian Postal Service (NIPOST) ta fito da shi, duk kamfanin da ke zirga-zirgar isar da saƙo a faɗin Najeriya zai biya naira miliyan 10 idan zai yi rajista sannan duk shekara ya biya miliyan huɗu.

Kamfanin da ke aiki a yankuna kuma zai biya miliyan biyar ne sannan ya biya biya miliyan biyu duk shekara.

Haka ma kamfanonin da ke aiki a iya cikin jihohi za su biya miliyan biyu don yin rajista, waɗanda kuma ke zirga-zirga a cikin birane za su biya miliyan ɗaya na rajista da kuma N400,000 duk shekara.


Wannan ya haɗa da duk wani kamfani da ke aikin karɓa da isar da saƙonni a Najeriya.

Facebook zai Samar da Internet Mai Arha a Africa

No comments:

Post a Comment