Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga matsayin mukaddashin shugaba hukumar EFCC, BBC ce ta ruwaito.
Mun kawo muku rahoton cewa mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.
Da misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ya kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami'an yan sandan sun yi awon gaba da shi daga fadar shugaban kasa.
Tuni Majiya ta bayyanawa The Nation cewa da wuya Magu ya tsira daga dakatar da shi.
"Hanashi komawa ofishinsa alama ce dake nuna cewa za'a dakatar da shi.
"Ya bayyana karara cewa fadar shugaban kasa ta kammala shirin neman sabon wanda zai maye kujerar." Cewar Majiyar.
Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da aka yiwa Ibrahim Magu
1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati
2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn
3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya
4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya
5. Ɓata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda hakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu
6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn
7. Ɓata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace
8. Fifita wasu jami'an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da 'Magu Boys'
9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba
10. Sayar da dukiyoyin sata ga yan'wansa, abokan arziki da abokan aiki.
No comments:
Post a Comment