Abubuwan da kuke bukatar sani a kan Ranar Hausa ta Duniya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Wednesday, August 26, 2020

Abubuwan da kuke bukatar sani a kan Ranar Hausa ta Duniya

Abubuwan da kuke bukatar sani a kan Ranar Hausa ta Duniya

Ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara ce ake bukukuwan Ranar Hausa ta Duniya.

Sama da Mutane Miliyan Saba'in ne ke Magana da Yaren Hausa a fadin Duniya wanda ya haura yawan mutanen dake ƙasar Ingila, Germany, Azrabijan da sauran su.

Taken bikin na bana shi ne "Bukatar Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar hada kan kasashen Afirka ta AU da ma Kungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS su mayar da harshen Hausa a matsayin na sadarwa a kungiyoyin."
  Babban kwani Æ™wararren Magini Wannan ranar dai ta samo asali ne a shekarar 2015 inda ma'aikacin sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su hadu su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21.

A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma'abota shafukan sada zumunta ke yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara.

Daga bisani kuma a shekarar 2018 aka fara gudanar da bukuwa na zahiri a gidan ɗan Hausa da wasu ƙasashe a fadin duniya kamar Ghana.


Babbar nasarar da za a ce Ranar Hausa ta Duniya ta haifar ita ce haÉ—a kan al'ummar Hausawan duniya a duk inda suke. A shekarar da ta gabata, an gudanar da bikin Ranar Hausa a kashe 17, cikinsu har da Faransa da Saudiyya.

Hausawa na haduwa a wannan rana domin sada zumunci da kuma tattaunawa a kan yadda za su taimaka wa juna.

A wannan shekarar "ana sa rai za a gudanar da bikin a ƙasashe sama da 25", in ji Abdulbaki Jari.

Akwai Hausawa da ke zaune a Sudan masu dimbin yawa

Masana harshe da dama na yi wa harshen Hausa kallon wani harshe mai yaduwa a fadin duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ce harshe na 11 a fadin duniya wajen masu amfani da harshen kuma na daya a Afirka ta yamma.

Sai dai akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin harshen Swahili da ake yi a kasashe da dama na yankin Afirka maso gabas ya dara na Hausa wanda ake yi a yankin Afirka ta yamma da Afirka ta tsakiya da ma kusurwar Afirka.

Sai dai nazarce-nazarce sun nuna harshen Hausa yana gaba da na Swahili ta fannin yawan masu yin yaren inda ita shi kuma Swahili ke gaba wajen yawan kasashen da ake yin yaren.

Tuni dai manyan kafafe irinsu Facebook da Google suke amfani da harshen Hausa inda tuni manhajar amfani ta Android da IOS suka shigar da shi cikin harsunan da yake amfani da su.

Ko a baya-bayan nan sai da hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaba domin yaki da annobar korona a Afirka.

Wadanda suka ƙirƙiro wannan ranar sun ce sun yi haka ne domin tuna wa da al'ummar Hausa game da muhimmancin harshen da yadda za a ciyar da shi gaba.

Sannan kuma ranar ta kasance a matsayin wata rana da ake ƙalubalantar al'ummar Hausawa domin fiddo da sabbin bincike da nazarce-nazarce domin habbaka harshen na Hausa.
                     Sarkin Rumfa
 Ana fatan harshen Hausa zai samu karbuwa nan ba da jimawa ba cikin harsunan amfani na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar hada kan Æ™asashen Afirka ta AU da ma Kungiyar Æ™asashen yammacin Afirka ta ECOWAS.

Iyaka dai har yanzu ana bukatar bincike sosai da nazari a kan harshen Hausa ta hanyar sabbin kirkire-kirkire na zamani domin daga martabar harshen.

No comments:

Post a Comment