Amnesty International ta ce Ƴance fashin daji sun kashe mutune 1,126 a wata shida - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, August 24, 2020

Amnesty International ta ce Ƴance fashin daji sun kashe mutune 1,126 a wata shida

Amnesty International ta ce Ƴance fashin daji sun kashe mutune 1,126 a wata shida a arewacin Najeriya

Amnesty ta ce sai bayan an kai hari jami'an tsaro ke zuwa


Kungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty Intanertional ta ce ƴan bindiga masu fashin daji sun kashe kimanin mutum 1,126 a jihohin arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.


A rahoton da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin, ta ce ɗaruruwan mutane ne aka raba da gidajensu a jihohin Kaduna da Neja da Katsina da Filato da Taraba da kuma Zamfara inda aka ƙone gidaje aka kuma sace mutane.


Amnesty ta ce tun 2016 take bibiyar matsalar ƴan bindiga masu fashin daji da kuma rikicin makiyaya da manoma.


Ƙungiyar ta ce hukumomin Najeriya sun bar mutanen karkara a hannun ƴan bindiga da suka kashe ɗaruruwan mutane, wanda kuma ke ƙara haifar da tsoro da fargaba kan wadatuwar abinci a yankunan karkara.


Hukumomin Najeriya da suka musanta rahoton Amnesty, zuwa yanzu ba su fitar da wani martani ba game da rahoton ƙungiyar.


Amnesty ta ce ta tattara bayanan rahotonta ne bayan tattaunawa da mutane a Kaduna da Katsina da Neja da Filato da Sokoto da Taraba da kuma Zamfara, waɗanda suka shaida mata cewa an bar su suna rayuwa cikin fargaba da tsoron hare-hare da garkuwa da su yayin da matsalar tsaro ta ƙara ƙamari a yankunan karkara.


 Yawancin waɗanda aka yi hira da su sun ce sai bayan awanni da harin da ƴan bindiga sannan jami'an tsaro ke zuwa duk da ana sanar da su cewa an kawo hari," inji rahoton na Amnesty.


Ta ce kuma "Wani hari da aka kai a Unguwan Magaji a jihar Kaduna, jami'an tsaro da suka zo suka ga irin makaman da ƴan bindigar suke ɗauke da su sai suka tsere. Daga baya da suka dawo, akalla mutum 17 aka kashe."


Amnesty ta ce ta tattara bayanai kan yawan hare-hare da satar mutane da aka yi a jihohi da dama na arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya a 2020.


Ta kuma ce kudancin Kaduna ne mafi muni inda ƴan bindiga suka kashe aƙalla mutum 366 a wasu jerin hare-hare tsakanin Janairu zuwa Yulin 2020.

Ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda ba a hukunta masu yin wannan kashe-kashen. 


"Yadda babu wani da aka hukunta kamar rashin adalci ne ga mutanen karkara waɗanda suke jin an fallasa su, in ji Osai Ojigho shugaban kungiyar Amnesty a Najeriya.


Amnesty ta kuma ce duk da matakan da gwamnatocin arewa ke ɗauka kamar kafa dokar hana fitar dare amma hakan bai dakatar da hare-haren da ƴan bindiga ke kaiwa ba kusan a kullum, inda ta ce hare-haren sun tilasta wa manoma tsere wa daga gidajensu da gonakinsu a wasu yankuna na Katsina.


"A Katsina akalla mutum 33,130 aka raba da gidajensu waɗanda suka warwatsu a sansanoni wasu kuma sun koma wajen ƴan uwansu a birane. Daruruwan manoma sun kasa yin noma a daminar 2020," a cewar rahoton Amnesty.


Haka kuma rahoton ya ce akalla mutum 380 aka sace domin neman kudin fansa a Kaduna da Neja da Nasarawa da Katsina da Zamfara, yawancinsu mata da yara.


Amnesty ta yi kira ga hukumomin Najeriya su ƙaddamar da bincike kan waɗannan kashe-kashe tare da tabbatar da an gurfanar da waɗanda suka aikata.


"Yawan kashe-kashe alama ce ta gazawar hukumomi kan haƙƙinsu na kare rayukan mutane.


 Ƙaruwar kashe-kashe a arewacin Najeriya ya nuna gazawar gwamnati


No comments:

Post a Comment