Sojojin Najeriya za su fatattaki ƴan Al Qa'eda – Enenche
Kodinatan yaɗa labaran rundunar Sojin Najeriya John Enenche, ya bayyanawa ‘yan Najeriya cewa su kwantar da hankalinsu bisa cewa da aka yi wai ‘Yan Al-Qida na kwararowa Najeriya.
Enenche ya ce wannan magana kamar shawara ce aka ba Najeriya da yaba yadda take ragargazar yan-ta’adda da suka ke a Najeriya.
Wannan abu ba abin a tada hankali bane. Zaratan sojojin Najeriya ba a kwance suke ba. A shirye suke.
Ba tun yanzu ake ba mu irin wannan shawarwari ba, kuma ai kuna ganin akan kama ko kashe wadanda ba yan kasar nan bane a hare-haren ‘yan ta’adda da sojojin ke kai musu.
A ƴan kwanakin nan a jihar Neja dakarun mu sun damƙe wasu da ba ‘yan Najeriya da ke aikata ta’addanci a kasar nan. Muna nan idanuwan mu a buɗe ƙulu-ƙulu, ba tsoro ba ja da baya.
Wata sabuwar ƙungiyar ƴan tawaye ta ɓulla a Kamaru
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/sabuwar-kungiyar-mayaan-taaddanci-ta.html?m=1
Enenche ya kara da cewa zuwa yanzu an samu gagarimar nasarori a wajen yaki da Boko Haram da ta’addanci a kasar nan, sauran ‘yan ɓurɓushi ne da ba a rasa ba. “Kuma suma mun ƙusa mu tarkata su.
Idan ba a manta ba Wani Kwamanda a rundunar sojojin kasar Amurka Dagvin Anderson da ke aiki a yankin Afrika ya gargadi gwamnatin Najeriya cewa kungiyoyi irin su Al-Qida na kwararowa yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Yanzu haka suna samun matsuguni da gudanar da ayyukansu a yankin Arewa Maso Gabas, Musamman yankunan Barno.
Yanzu kuma sun fara kafa sansanoni a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Jihohin Arewa Maso Yamma sun hada da, Kaduna, Kano, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina da Jigawa.
Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro umarnin sabunta dabarun yaƙar ta'addanci
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/buhari-ya-baiwa-hafsoshin-tsaro-umarnin.html
Zamu hada kai da Najeriya domin mu rika sanar da juna bayanan sirri game da yadda wadannan kungiyoyi ke kokarin mamaye Najeriya.
Kungiyoyi kamar su Al-Qida, Boko Haran, ISIS, da ISWAP. Za mu rika raba bayanan sirri a tsakanin mu domin sanin yadda za a tunkare su.
Babu wata ƙasa da zata zo ta yi wa Najeriya yaki.
Dole dai Najeriya ce zata yi wa kanta abinda ya dace ko, Kasar Amurka, Britaniya, da wasu kasashe na Turai duk sai dai su taimaka mata amma ita ce wuka ita ce nama a wannan aiki.
Dole sai mun fahimci mene Najeriya ke so mu taimaka mata da shi. Daganan sai gaba dayan mu, mu tsara yadda za mu tsara abubuwan.
Najeriya shirgegiyar kasa ce, dake da iyakoki da ƙasashe a zagaye da ita. Dole ta maida hankali wajen yin amfani da jiragen yaƙi na sama idan tana son daƙile hare-hre da kwararan ‘yan kungiyoyi.
Gwamna Zulum ya ce Sojoji suka Kai Masa Hari ba Boko Haram ba
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/gwamna-zulum-ya-tona-asirin-waanda-suke.html?m=1
No comments:
Post a Comment