Tsohon sarki Sanusi na II zai fara koyarwa a jami'ar Oxford - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, August 13, 2020

Tsohon sarki Sanusi na II zai fara koyarwa a jami'ar Oxford

Tsohon sarki Sanusi na II zai fara koyarwa a jami'ar Oxford

Jami'ar Oxford dake Birtaniya ta tabbatar da matsayin baiwa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanudi na II damar zama malami a cikin ta wanda zai fara aiki daga watan Oktoba mai zuwa.

Sanarwar da jami’ar ta gabatar ya nuna cewar Tsohon Sarkin zai yi aiki ne a Sashen dake nazarin tarihin Afirka da kuma kwalejin Anthony dake cikin makarantar.

Sanarwar tace tuni kwamitin gudanarwar Jami’ar ya amince da bukatar Mai Martaba Tsohon sarkin na bada gudumawa a kakar karatu mai zuwa na shekarar 2020 zuwa 2021.

Jami’ar tace Sarki Sanusi mai murabus zai yi amfani da wannan dama wajen rubuta littafi akan ‘yadda Babban Banki ya taka rawa wajen matsalar tattakin arzikin duniya wanda zai mayar da hankali kan Babban Bankin Najeriya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013.

Jami’ar tace binciken zai baiwa Sarkin damar gabatar da kwarewar da ya samu lokacin da ya jagoranci Babban Bankin Najeriya a matsayin sa na Gwamna da kuma Masani.

Tsohon Sarkin ya jagoranci Babban Bankin Najeriya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014.

No comments:

Post a Comment