Anyi Ram da Mutanan da Suka wawashe Abincin Gwamnatin a Abuja - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, October 26, 2020

Anyi Ram da Mutanan da Suka wawashe Abincin Gwamnatin a Abuja

 


Anyi Ram da Mutanan da Suka wawushe Abincin Gwamnatin a Abuja


Ministan babban birnn tarayya Abuja Malam Muhammad Bello ne, ya bayar da umarnin kama ma su barnar da suka balle babban shagon kayan abinci da ke unguwar Gwagwalada tare da gurfanar da su a gaban kotu.


Ministan ya bayar da wannan umarni ne yayin taron gaggawa da ya gudanar da shugabannin hukumomin tsaro na Abuja a ranar Litinin.


Ministan ya bukaci mabarnatan su gaggauta dawo da kayan da suka kwashe a yayin da yake sanar da cewa an baza jami'an tsaro domin kare sauran manyan shaguna da ke rukunin masana'antu da ke Idu.


A cewar Ministan, abinda yake faruwa yanzu ba zanga-zangar ENDSARS bace, sata ce da 'yan iskan gari ke yi.


A nata bangaren, karamar ministar Abuja, Dakta Ramatu Aliyu, ta yi Alla-wadai da abinda ya faru cikin kakkausar murya


Ministar ta ce babu wata kasa da zata rayu ba tare da ma'adanai na abinci ba irin wadanda yanzu mabarnata ke ballewa suna kwashe abincin ciki.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

No comments:

Post a Comment