Najeriya ta sanar da Ranar Bude Makarantu
Ma'auratar Ilimi ta Najeriya ta ayyana 12 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a bude makarantu a duk fadin kasar bayan da aka kwashe sama da wata shida makarantun na kulle sanadiyyar annobar COVID-19.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya sanar da umurnin bude makarantun yayin wani taron manema labarai da ya kira a ranar Juma’a inda ya bayyana cewa za a bude daukacin makarantun hadin kai na "Unity Schools" a wannan rana.
Ma’aikatar ilimin ta ce ta dauki wannan matakin ne, bayan da ta nemi shawarar kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da annobar COVID-19.
Adamu ya kuma kara da cewa, za a tabbatar da cewa makarantun sun bi ka’idojin da gwamnati ta gindaya domin kare lafiyar dalibai da malamai.
Domin siyan DATA Ta MTN 1GIG AKAN 350 yi magana ta WhatApp 08122225296 ko Kira 08109671936
Kafafen yada labarai da dama sun ruwaito Ministan yana cewa, makarantun jihohi da na masu zaman kansu, su kintayi lokacin da yafi musu don bude nasu makarantun.
Najeriya na da makarantun hadin kai na Unity 104.
Mallam Adamu ya kuma yi gargadin cewa gwamnati za ta rufe duk makarantar da aka samu da laifin bijirewa ka’idojin da gwamnati ta gindaya musamman idan aka samu bullar cutar a makarantar.
Mutum 59, 001 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, 1,112 sun mutu bisa alkaluman da hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC ta fitar a ranar Alhamis.
Shugaban Amurka Donald Trump da matar da sun kamu da cutar korona
https://www.arewagist.com.ng/2020/10/trump-da-matar-da-sun-kamu-da-cutar.html?m=1
No comments:
Post a Comment