Sufeton Ƴan Sandan Ya Haramta Wa Rundunar SARS Kafa Shingayen Bincike - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, October 4, 2020

Sufeton Ƴan Sandan Ya Haramta Wa Rundunar SARS Kafa Shingayen Bincike

 


Sufeton Ƴan Sanda Ya Haramta Wa Rundunar SARS Kafa Shingayen Bincike.


Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya haramta wa runduna ta musamman mai yaƙi da fashi da makami da ake kira SARS da sauran ɓangarorin rudunonin ƴan sanda kafa shingayen bincike.



Cikin sanarwar da  rundunar ta wallafa a shafin Twitter a wasu jerin sakonni Ranar Lahadi, sufeton ƴan sandan ya haramta wa dukkanin rundunoni na musamman da suka haɗa da FSARS da STS da IRT da ke yaƙi da ƙungiyoyin asiri kafa shingayen bincike domin tarewa da binciken ababen hawa.


Sannan an haramta wa duk wani jami'in ɗan sanda fitowa da kayan gida ba tare da kayan ƴan sanda ba. 


Taba link kakalli yadda ƴan Sandan Suka kashe mutum, kuma suka sace motar sa

https://youtu.be/gnSfWeQJGDQ



Sanarwar ta ce wasu jami'an na fakewa da wannan suna yin abubuwan da ba su dace ba da suka saɓa doka.



Babban Sufeton ƴan sandan ya kuma yi gargaɗi ga rundunonin game shiga haƙƙin sirrin rayuwar mutane musamman binciken wayoyins mutane na salula da kwanfuta da sauran na'urori ba tare da wani samun izini ba.



Sanarwar ta ce an kama wasu daga cikin jami'an SARS da ake zargi da cin zarafin mutane a Legas, sannan za a ci gaba da bincike kan zargin cin zarafi da wasu jami'an rundunar SARS suka aikata.



An buƙaci jami'an su mayar da hankali ga laifukan da suka shafi fashi da makami da satar mutane da sauran muggan laifukan da aka kafa rundunonin domin su, ba su koma cin zarafin al'umma ba.


No comments:

Post a Comment