Ire Iren Kasuwancin Cryptocurrencies - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, May 9, 2021

Ire Iren Kasuwancin Cryptocurrencies


 Tsarin Kasuwancin Crypto ya kasu kashi biyu, a karkashin ko wanne sashe Akwai nasa bangarorin, akwai Trading wato cinikayyar yau da kullum, shine ka sayi Coin yau gobe ka siyar, sannan kuma akwai Investing shine cinikayyar da ake daukar dogon zango, ita mutum idan ya siya sai ya bayan wani lokaci yayi daraja sai ya siyar. Ga cikakken Bayanan su:

KASUWA TA YAU DA KULLUM MA'ANA "TRADING"

Ita wannan ta ƙunshi wasu hanyoyin da suke da bukatar cikakken lokacin mutum da kuma natsuwar sa domin akoda yaushe ana gudanar da siyen da sayarwa a kasuwa, kamar dai yanda masu shaguna suke ko masu yawan talla idan suka siyo a farashi to sai su tafi wata kasuwar inda zasu sayar su sami Riba akan yanda suka siyo. Misalin su sun hada da:

1. Day Trading: Shine Wanda Mutum zai shiga kasuwa a rana daya ma'ana a cikin kwana É—aya zasu zuba kudin su kuma zasu cire su duka, to dama sun nazarci kasuwar cewa akwai wasu awanni da take bada Alkhairi, sai su Saita kafin wannan lokacin su shigar da kudin su da zarar lokaci ya tawo sai su kwashe kuÉ—in su su fita.


To a Crypto Akwai masu irin wannan tsarin da suke shiga kasuwa kuma su fita a tsakanin awa 24 (kwana É—aya), wanda su irin wadannan suna aiki ne da yanayi da suka lura cewa a rana akwai wani lokacin Wani coin yafi tashi. 


Shi irin wannan tsarin yana kawo Riba sosai, amma Mafi yawancin lokuta Irin wannan tsarin kasuwar yana da hadari, saboda haka idan mutum ba kwararre bane to ba'a bashi shawara yayi amfani dashi.


2. Trend Traders: wadannan suna amfani da irin yanda kasuwa take jan hankali, kuma ba'a cika rike coin sama da wata daya a wannan tsarin domin da zarar ya daina Trending to sufa ba Magana.


Saboda haka su irin wadannan suna daukar idan suka ga Coin Yana Trending a kasuwa da sauran kafafen yada labarai to sai su siya kuma su rike shi a hannun su, haka gwargwadon lokacin da ya dauka yana Trending a media, haka kuma idan baya Trending Sosai Shima Zasu shiga cikin kankanen lokaci gwargwadon faduwar da yake tayi.


Irin wannan tsarin zaka iya Shawartar sabon shiga, wanda yasan yana da kula da yanayin Trending na Coin a Kasuwa.


3. Swing Trading: shi Kuma wannan tsarin yana a tsakanin na farko ne (day trading) dana biyu wato (trend trading) Wanda galibi ba'a rike coins sama da sati Daya ko biyu. Kuma wannan shi ne kusan wanda aka fi so dan koyo ya lazumta domin zai bashi cikakken ikon lura da kuma koyon yanda kasuwa take garawa ba tareda ya fuskanci matsalar asara mai tsanani ba.


4. Scalping: shi wannan tsarin yafi ko wanne sauki, masu irin wannan Kasuwancin babu ruwansu da wani haw-hawa da kasu takeyi ko kuma wata faduwar da kasuwa takeyi, su suna bi ne a hankali, sannu sannu.


Sannan idan mutum ya iya irin wannan Kasuwancin to hankalin sa bai cika tashi ba, yana kasuwar sa ne da juya ribar sa da kadan-kadan, mafi yawancin wannan tsarin na kwararru ne domin su hankalin su baya tashi na idan sunga wani coins ya hau 100% lokaci guda ko kuma ya fadi warwas lokaci guda. Kuma wannan Kasuwancin bana kanana bane masu koyo, yafi dacewa ga manyan yan kasuwa, Suna amfani da cin yar karamar Riba amma kuma a dade ana gudanar da kasuwar.


Kamar yanda yanzu Bitcoins yake idan Kana da yan kananan kudi to ba'a Shawartar mutum ya fara dashi domin zai jima bai ci wata Riba ba, in Kuwa mutum mai kudi ne sosai da zai zuba miliyoyi to za'a Shawarce sa da ya sayi Bitcoins.


2 KASUWA TA DOGUWAR AJIYA "INVESTING"

Kasuwar da ake investment ma'ana zuba kudin ake a rika lura tare da duba yanayin kasuwa wajen sanin inda take nufa kamar yanda zaka sayi Coins din da zaka zuba kudinka wanda ake sa ran bayan wani lokaci zaka dawo ka kwashi ribar kuÉ—in ka mai yawa ma'ana ya tashi kenan, Sabanin kashin farko wanda yake kamar yanayin Kasuwancin yau da kullum na ka siya kuma ka siyar da zummar samun riba. Ire-iren wannan sune:


1. Buy and Hold: Iya Wannan alamar yanda sunan yayi ishara shine Mutum ya siyi Coin Sannan ya rike shi ma'ana ya ajiye zuwa wani dogon lokaci, ba tare da duban Yanayin haw-hawa ko sauka da kasuwa takeyi ba.


Misalin irin wannan tsarin shine Lokacin da kayan gona suka zo to gaba daya zaka samu sunyi araha sun fadi a kasuwa, to shi kuma Wanda yake da kudi zai iya fito dasu ya siya ya ajiye zuwa wani lokaci idan sukayi tsada babu su a kasuwa ya fito dashi ya sayar.


Saboda haka, a Crypto ba Kowanne Coin ne zaka siya kuma kace zakai masa doguwar ajiya ba domin kana iya siya kuma azo ya rufta dakai musamman ma irin shitcoins dinnan.


DAGA KARSHE.

Yana da Kyau mu sani cewa zabar tsarin da zaka tafiyar da kasuwancin Crypto din ka ba Abu ne mai sauki ba wanda zai dace da dukkanin irin bukatun da kai kake sakawa kanka. 

Saboda haka domin samun tsarin da zai dace dakai Sai ka bibiyi Yanda kowanne yake tasiri a kasuwa domin samun wanda ya dace da muradan ka.


Amma fa ka sani cewa sanin Plan din da zaka dora kasuwar ka akai ba wai yana nufin cewa shi kadai zaka Makalewa ba, bayan wani lokaci kana kara fahimta da Gogewa to kana dada sanin yanda zaka gudanar da kasuwar ka, zaka riƙa sassauya Plan dinka kuma kana yi masa gyara yanda zai dace maka da kasuwa. Idan ma ka fahimci abin yanda ya kamata to duk zaka iya zama kowanne daga ciki ka riƙa sassauya wa gwargwadon yanda kasuwa ke tafiya.


Wadannan sune hanyoyin da mutum zai bi domin aiwatar da Kasuwancin sa ba tareda ya dinga samun matsalar asara da faduwa ba (duk da cewa akwai kaddara...), Kasuwancin Crypto Jami'a ce ta Kasuwancin da kullum koyarwa take ga dalibanta. Kai Dalibin Crypto ka Tsaya kaima kanka tanaji me kyau domin Muddin Allah yasa ka rabauta da wannan Kasuwancin to Wallahi Allah ya rufa maka asiri.

By Mustapha Gfatu


Ina Siyar da USDT da classic coin, me bukata yamin magana 08122225296



No comments:

Post a Comment