[[Ka karanta]] Shin bauɗewar babban yatsan ƙafa gado ne? - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, April 8, 2019

[[Ka karanta]] Shin bauɗewar babban yatsan ƙafa gado ne?

Shin bauɗewar babban  yatsan ƙafa gado ne?
Karkacewar ko bauɗewar babban ɗan yatsan ƙafa na daga cikin matsalolin da kan shafi tafin sawu. Wannan matsala na faruwa a yayin da babban ɗan yatsan ƙafa ya karkace zuwa ɗan yatsa na biyu sakamakon canje-canje a tantanin da ke riƙe da ƙasusuwan babban ɗan yatsan.Sai dai wannan matsala an ta fi bayyana ga mata. 

Daga cikin abubuwan da ke kawo matsalar sun haɗa da:

1] Gado: Kaso mai yawa na masu bauɗaɗɗen ɗan yatsan ƙafa suna samo shi ne ta hanyar gado daga ɓangaren uwa ko uba. Haka nan masu shimfiɗaɗɗen tafin sawu  wato "Flat foot" a turance na da ƙarin haɗarin samun bauɗaɗɗen babban ɗan yatsan ƙafa.

2] Bayan samun wannan matsalar ta hanyar gado, ana samunta  ta hanyar sanya matsatstsen takalmin da yake matse 'yan yatsun ƙafa, misali, takalmi coge. Sanya irin waɗannan takalma yau da gobe kan kawo canje-canje a tantanai da tsokokin da ke riƙe da babban ɗan yatsan. Saboda haka akwai buƙatar sanya takalmin da ke da yalwataccen masakar 'yan yatsun ƙafa.

3] Ciwon kumburin gaɓɓai kamar ciwon amosanin gaɓa, ciwon sanyin ƙashi, ciwon gawut, da sauransu.

Alamomin bauɗewar babban ɗan yatsan sun haɗa da:

1) Bauɗewar babban ɗan yatsan zuwa yatsa na biyu.

2) Bayyanar kanta, wani lokacin tare da kumburi, a gefen maɗaukar babban ɗan yatsan.

3] Ciwo tare da kumburi a dai-dai kantar  babban yatsan.

 A yayin da kike/kake fama da irin wannan ciwon ɗan yatsa tuntuɓi likitan Fisiyo domin dubawa da bada shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar.

No comments:

Post a Comment