Yadda ake war-ware sihiri - Daga Babban Malami Dr Isah Ali Pantami. - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, April 6, 2019

Yadda ake war-ware sihiri - Daga Babban Malami Dr Isah Ali Pantami.

Yadda ake war-ware sihiri -

Daga Babban Malami Dr Isah Ali Pantami.

1) A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan.

2) Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan.

3) Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara).

4) Sai a karanta Suratul A'araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.

5) Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82.

6) Suratul Kafirun kafa daya

7) Falaki da Nasi kafa uku- uku.

8) Sai a karanta wannan addu'a
"Allahumma rabban-nas az'hibil ba'as ashfi wa antash-shafi la shifa'a illa shifa'uk shifa'un la yugadiru sakaman" kafa uku.

9) Sannan za'a iya karawa da wannan addu'a "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika" kafa uku

10) Insha Allahu ta'ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi.

Basai mutum yaje wajen boka an danfare shi ba.

Kamar yadda Malam yake fadi basai an maka/ miki sihiri ba, mutum zai iya yi domin tsima jikin sa daga shairin masharranta.

AYATUSH~SHIFAA
surorin qur,ani guda shida dake karya sihir ko asiri.

1.sur,atul  tauba:ayata   14.
2.sura,ratul    yunus ayata   57.
3.sura,atul    nahli:ayata   69.
4.sur,atul      isra,i:ayata   82.
5.sura,atul      shu,ara:ayata  78~82.
6.sura,atul      fuslilat:ayata    44


dan allah idan kaima akaturoma kai kokari katurawa sauran yan,uwa muslimi kai ma kasamu naka ladan.allah yasa mudace ameen.

No comments:

Post a Comment