Gwamnatin Tarayya ta bawa jigawa takin zamani da kayan tallafi Tirela 150 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, June 6, 2020

Gwamnatin Tarayya ta bawa jigawa takin zamani da kayan tallafi Tirela 150


 Gwamnatin Tarayya ta bawa jigawa takin zamani da kayan tallafi Tirela 150

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da rabon takin zamani ga manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2018 a jihar Jigawa.

Da take ƙaddamar da shirin Ministar ma'aikatar jinkai da ta bada tallafi Hajiya Sadiya Umar Farouk ta ce jihar Jigawa, jihar manoma ce, da tayi  fice wajen samar da abinci ga al'ummar kasar nan.

Hajiya Sadiya Farouk ta bayyana cewa an samar da takin kimanin trok dari tara da hamsin inda tace trok dari shida, biyar  sun iso jihar Jigawa domin raba wa ga manoma.

Tace wannan na cikin kokarin da Gwamnati ke keyi domin ganin an tallafawa manoman da ambaliyar tayiwa barna.

Ministar ta Kuma yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa irin jajircewasa Musamman abubuwan da suka shafi al'ummar sa.
Daga bisani tayi kira ga manoman da za su amfana da takin da suyi amfani dashi domin bunkasa nomansu.

Da yake jawabi gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya yabawa ministar bisa kokarin datake na ganin ta kyautata rayuwar masu karamin karfi.

Yace jihar Jigawa ta fuskanci ambaliyar ruwa wacce aka samu salwantar kayayyakin gona a shekarar 2018 inda yace Gwamnatin tarayya ta bada daukin gaggawa ga jihar.

A wani labarin kuma Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da kayan tallafi ga Jihar Jigawa wanda yakai tirela 150 domin rage radadin cutar korona.

Gwamna Badaru Abubakar ya kuma godewa shugaba Muhammad Buhari bisa kulawar da yake wa harkar noma a fadin kasar nan.



No comments:

Post a Comment