Ganduje ya Raba gidajen Ruga Kyauta ga fulani Makiyaya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, June 6, 2020

Ganduje ya Raba gidajen Ruga Kyauta ga fulani Makiyaya

Ganduje ya Raba gidajen Ruga Kyauta ga fulani Makiyaya

Mai Girma Gwamna, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya Jagoranci kaddamar da rabon gidaje Ruga kyauta domin inganta harkokin kiwo da rayuwar fulani makiyaya a fadin Jihar Kano, wanda aka gabatar a dajin Dan soshiya dake Karamar Hukumar Kiru Karkashin Kwamitin duba wajen tabbatar da RUGA da Kasuwar Nono Karkashin Dr Jibrilla Muhammad.

Gwamna Ganduje ya ce kasancewar sa bafulatani Makiyayi kafin kasancewar sa Gwamnan yazama lallai ya tallafawa makiyayan wanda hakan zai inganta rayuwar su data ya yansu.

A yau an fara rabon gidaje 25 da aka kammala daga cikin gidaje 200 wanda Gwamnatin zata gina a wannan daji Sannan anyi rijiyoyin burtsatse don Shan ruwan shanunsu, a gurare 5 cikin dajin tare da aikin gina Dam wanda aikinsa ya tsaya saboda damina.

Cikin abubuwan da za'a gina a wannan daji sunhada da makaranta da asibitocin mutane dana dabbobi domin inganta rayuwar su da magance rigingimun makiyaya da masu satar shanu.

Gwamna yasamu rakiyar Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinonin Ruwa, Ilimi, Yada Labarai, Daraktan Tsaro na Fadar Gwamnati Col Umar Malami.

No comments:

Post a Comment