Majalisa ta gayyaci shugabannin NNPC, CBN, FIRS, da wasu domin bincike kan kashe-kashen kudi - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, June 18, 2020

Majalisa ta gayyaci shugabannin NNPC, CBN, FIRS, da wasu domin bincike kan kashe-kashen kudi

Majalisa ta gayyaci shugabannin NNPC, CBN, FIRS, da sauransu domin Bincike kan kashe-kashen kudi

Majalisar Wakilai ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da kuma Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kolo Kyari.

Haka kuma Majalisar ta gayyaci Shugaban Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali, domin su yi bayani filla-filla game da duk wani shige-da-ficen kudi a ma'aikatun da suke jagoranta.

An gayyaci shugabannin hukumomin gwamnatin tarayyar ne saboda sun ki bayar da bayani yayin da ofishin Odita-Janar na Tarayya ya nuna rashin gamsuwa da yadda suke kashe kudade.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa, shugabannin hukumomin gwamnatin sun ki yi wa ofishin Odita-Janar na Tarayya bayanin yadda suke kashe kudade duk da ya nemi bukatar hakan.

Sauran wadanda ake sa ran za su bayyana a gaban kwamitin bin diddigin kudi na majalisar sun hadar da:
Shugaban Hukumar FIRS; Mohammed Nami
Shugaban Hukumar da ke sa ido kan kayyade albashin manyan jami'an gwamnati; Elias Mbam;

Daraktan Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya DPR; Sarki Auwal;

Babban Sakataren Hukumar kayyade farashin man fetur PPRA, Abdulkadir Saidu;
Shugaban Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA); Uche Orji;

Shugaban Kamfanin sarrafa iskar gas na NLNG, Tony Attah;
Shugabannin Hukumar Kula da Shirin gwamnatin Tarayya na rage radadin janye tallafin man fetur wato Sure-P;

Manyan Sakatarorin dindindin na Ma'aikatar Kudi ta Tarayya; Dr Mahmoud Isa-Dutse; Dr Muhammed Dikwa; Mr Ernest Umakhir.

Babban Sakataren dindindin na Ma'aikatar hako Ma'adanai ta Tarayya; Dr. Abdulkadri Mu'azu;

Shugaban Hukumar hako Ma'adanai; Engr. Obadiah Simon Nkom.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban kwamitin bin diddigin kudi na majalisar, Wole Oke, shi ne ya gabatar da takardun goron gayyatar manyan jami'an gwamnati da har yanzu ba su amsa ba.

Mista Oke yayin zaman tattaunawa kan binciken kashe-kashen kudi da Odita-Janar na tarayya ya gabatar, ya gargaÉ—i manyan jami'an gwamnatin da aka gayyata .
Ta ce "'Yan Najeriya sun cancanci sanin abin da yake faruwa da kudadensu."

No comments:

Post a Comment