Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ya kamata a sake zama a tattauna irin yawan kudaden da ake barnatarwa akan manyan jami'an gwamnati a kasar nan.
Ya ce abin na da wuya saboda wadanda zasu yi gyaran na amfana da yanayin; amma dai wajibi ne a san na yi.
Osinbajo ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyin tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, a taron yanar gizon da Cocin Emmanuel ta shirya kan makomar tattalin arzikin Najeriya idan COVID-19 ta wuce.
Sanusi yace: "Jihar Atalanta (a Amurka) na da GDP wanda ya fi na Najeriya, kuma fa ba Atlanta bace jiha mafi arziki a Amurka."
"Cinikin da kamfanin Tesla ke yi a shekara ya fi kasafin kudin Najeriya, shin ba ka tunanin ya kamata mu rage yadda muke barnatar da kudi; shin bai kamata mu sake duba wannan kundin tsarin mulkin ba da kanta."
"Misali a mayar da aikin majalisa na wucin gadi, a mayar da Majalisa daya maimakon biyu, a mayar da kananan hukumomi karkashin wata ma'aikata daban?"
A martaninsa, Osinbajo yace: "Ko shakka babu muna yin wani irin gwamnati mai tsada, amma kamar yadda ka sani, duba ga wannan kudin tsarin mulkin, wadanda ya kamata su rage abin, musamman, a mayar aikin majalisa na wucin gadi sune yan majalisa."
"Saboda haka zai yi wuya a samu wani nasara idan aka bukacesu su canza abinda suke matukar amfana dashi."
"Saboda haka akwai bukatar kasar nan ta sake zama na musamman akan lamarin nan kuma ya kamata mu tabbatar da cewa bamu barnatar da dukiyar da ya kamata a ciyar da kasa gaba dashi, wajen biyan alawus."
"A yanzu kashi 70% na kudin shigarmu alawus ake biya dasu , saboda haka ko shakka babu ya kamata a rage."
No comments:
Post a Comment