Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Adams Oshiomhole, ya ce ya amince da rushe kwamitin kolin jam'iyyar, wanda yake jagoranta gabanin dakatar da shi da majalisar koli ta yi.
Wannan ne karon farko da tsohon shugaban ya yi magana kan rikice-rikicen jam'iyyar wadanda suka janyo rushe kwamitin kolin.
Tsohon shugaban ya ce ba ya nadama kan dukkan abubuwan da ya aiwatar lokacin da yake jagorantar kwamitin, ya kuma yi alkawarin ci gaba da nuna goyon bayan tare da biyayya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Oshiomhole ya ce sakamakon umarnin shugaba Buhari na cewa duka 'ya'yan jam'iyyar su janye kararrakin da suka shigar gaban kotu, shi ma ya bai wa lauyansa umarnin janye ta shi karar kan ƙalubalantar dakatar dashi daga gaban babbar kotun daukaka kara ta kasar.
No comments:
Post a Comment