Jami'an tsaro sun ma maye gidan marigayi Ajimobi - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, June 28, 2020

Jami'an tsaro sun ma maye gidan marigayi Ajimobi

Jami'an tsaro sun ma maye gidan marigayi Ajimobi

 Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta tura jami'anta gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi. 

Gwamnatin jihar da musulmai basu amince da inda iyalansa suka zaba don binne mamacin ba. 

A lokacin da jaridar The Nation ta ziyarci wurin, ta samu motar 'yan sanda biyu, motar sintiri daya da kuma wata mota kirar Kia Rio wacce jami'an tsaron farin kaya suka ajiye a kusa da wurin. 

  Wasu majiyoyi sun ce tura jami'an tsaro da aka yi don mamaye wurin, baya rasa nasaba da rigimar da ake kan wurin da iyalan marigayi tsohon gwamnan suka zaba domin binne shi. 

Majiyoyi da dama sun kara da cewa, akwai yiwuwar an tura jami'an tsaron ne saboda a kiyaye dokoki ko kuma ta yiwu suna wurin ne koda iyalan mamacin za su matsa binne shi a masallacin. 

Duk Kokarin  zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya tashi a tutar babu. 

Sannan an tura mishi sakonnin karta kwana amma har lokacin hada wannnan rahoto bai mayar da amsa ba.

 A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne dai, Abiola Ajimobi ya rasu, a wani Asibiti a jihar Legas bayan fama da cutar korona. 

Sai dai kuma har zuwa yau Lahadi, 28 ga watan Yuni, ba a binne tsohon gwamnan ba, sakamakon rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar da iyalansa a kan wurin da za a binne gawarsa.

 Haka zalika wasu al’ummar Musulmi sun yi gargadi a kan shirin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo na binne shi a cikin masallaci. 

A baya bayan ne dai kakakinsa, Bola Tunji, ya sanar da cewa a za binne shi a babban masallacinsa da ke Oke-Ado a garin Ibadan, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni da karfe 12.00pm na rana.

 Wannan sanarwa ta tayar da kura yayin da wasu al'ummar musulmi suka tabbatar da haramcin yunkurin, bisa ga madogara ta shari'ar Musulunci.

 An tattaro cewa Musulmai a fadin Najeriya sun ce abinda iyalan marigayin ke kokarin yi na binneshi cikin Masallaci Haramun ne kuma hakan zai sa mutane su daina Sallah a Masallacin. 

No comments:

Post a Comment