PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, June 15, 2020

PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi

PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta sake yin tir gami da Alla-wadai dangane da yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan.

PDP ta yi zargin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa ta jam'iyyar APC sun yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi.

Jam'iyyar ta bayyana damuwa matuka dangane da yadda 'yan ta'adda ke zubar da jinin 'yan Najeriya a Katsina, Zamfara, Sakkwato, Borno, Kaduna, Kogi, Taraba da sauran sassa a fadin kasar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, PDP ta bayyana damuwarta cikin wata sanarwa da kakakinta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Lahadi cikin birnin Abuja.

PDP ta ce "tana jin radadin halin tsoro da zalunci da 'yan kasar nan ke fuskanta a hannun 'yan daban daji, masu tayar da kayar baya da kuma masu garkuwa da mutane a sakamakon gazawar gwamnatin APC."

Gwamnatin APC ta kasa sauke nauyin da rataya a wuyanta, ta gaza inganta tsaro ta hanyar tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al'umma."

"Babban abin takaici shi ne yadda gwamnatin APC ke ikirarin tana batar da kudi kan sha'anin tsaro amma kullum lamarin sai ci gaba da tabarbarewa ya ke."

“Abinda ya ma fi zama babban takaici shi ne yadda 'yan daban daji ke cin karensu babu babbaka sakamakon gazawar gwamnatin APC da har su ke iya kai hare-hare jihar Katsina da ta kasance mahaifar Shugaban kasa."

Muna kira ga 'yan Najeriya da su lura cewa, har kawo yanzu gwamnatin APC ta gaza yin bayani kan masu tayar da zaune tsaye da ta shigo da su daga kasashen da ke makwabta da Najeriya musamman Chadi da Jamhuriyyar Nijar domin su hana ruwa gudu yayin babban zabe na 2019."

Jam'iyyar mai hamayya ta ce gwamnatin APC ta gaza bijiro da matakai na kawo karshen masu tayar da kayar baya face bayar da sakonnin ta'aziya akai-akai bayan kowane mummunan hari da aka kai kan al'umma.

PDP ta janyo hankalin shugaban kasa da ya tashi ya farga "kuma ya farka daga baccinsa domin maido da tsarin ingantaccen tsaro a kasar."

No comments:

Post a Comment