Sanatoci sun maida lissafin kudin gangar man fetur zuwa dala $28 a kasafin wannan shekarar ta 2020 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Wednesday, June 3, 2020

Sanatoci sun maida lissafin kudin gangar man fetur zuwa dala $28 a kasafin wannan shekarar ta 2020

Majalisar Dattawa tana hasashen za a saida gangar man fetur a kan dala $28 

Sanatoci sun maida lissafin kudin gangar man fetur zuwa dala $28 a kasafin wannan shekarar ta 2020 

An kara kudin da ake sa ran samu ne saboda yadda kasuwa ke tafiya a yau Majalisar 
dattawan tarayyar Najeriya ta yi gyara game da hasashen da gwamnatin tarayya tayi kan kudin da ake sa ran za a samu daga man fetur a kasafin kudin shekarar nan mai-ci.

 Bayan zaman farkon da aka yi a makon nan, sanatocin Najeriya sun maida lissafin kowace gangar mai kan Dala $28. 

Gwamnatin tarayya ta tsaida lissafin ta kan Dala $25. 

An cimma wannan matsaya ne a ranar Talata, 2 ga watan Yuni 2020 bayan da shugaban kwamitin tattalin arziki, sanata Solomon Olamilekan ya gabatar da rahotonsa a majalisar.

 Ganin halin da ake ciki a yanzu na tabar barewar tattalin arzikin Duniya, majalisar ta bada shawarar tsaida farashin Dala a kan N360, sannan a guji karya darajar Naira a nan gaba. 

Har ila yau, majalisar ta tsaida danyen man da za a hako duk rana a kan ganguna miliyan 1.8

Sanata Solomon Olamilekan ya kuma yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara kokari wajen fadada hanyar samu da kara karfin tattalin arzikin Najeriya. 

An yi wadannan gyare-gyare ne a tsarin MTEF da FSP sakamakon karyewar farashin mai a Duniya a dalilin annobar cutar Coronavirus da ta shafi Najeriya da sauran kasashe.

 ‘Yan majalisar tarayyar sun yi kira na musamman ga hukumar mai ta kasa  NNPC data rage adadin danyen man da take hakowa, Wanda hakan ya zo daidai da yarjejeniyar OPEC. 

An kuma bukaci gwamnatin tarayya ta dage wajen samun kudin shiga ta hanyoyin haraji.

 Wannan kwamiti na majalisar dattawan ya yi magana kan toshe kafar facaka da kudin kasa. 

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya amince da duk shawarwarin da kwamitin ya kawo. 

Ya ce an kara kudin da aka yanke ne saboda ganin yadda mai ya fara tashi. 

No comments:

Post a Comment