SERAP ta kai karar Buhari Majalisar Dinkin Duniya kan Zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiyaalmundahan.
Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya, ta shigar da bukatar gaggawa zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya kan kwas kwarimar da aka yiwa kasafin kudin kasar nan na bana.
Kungiyar ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga lamarin, wanda take ganin hukuncin da Gwamnatin Najeriya ta yanke ya yi hannun-riga da dai-dai.
SERAP ta aike da kiran gaggawa zuwa ga wakilai 3 na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, tana kira dasu hanzarta sauya haramcin da aka aiwatar a kasafin kudin kasar nan na bana.
Ta ce akwai mafi kololuwar rashin daidaito na zaftare kasafin kudin sashen harkar ilimi da kuma na kiwon lafiya a sauye-sauyen da Gwamnatin Najeriya tayi wa kasafin kudin kasar.
Ta kuma yi kira ga wakilan Majalisar Dinkin Duniya dasu dakatar da Gwamnatin Najeriya da suke shirin batar da naira biliyan 27 wajen gyara gine-ginen Majalisar Dokoki ta Tarayya.
Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da SERAP ta nemi su shiga lamarin sun hadar da; Ms. Koumbou Boly Barry, mai lura da hakkokin ilimi; Mr. Dainius Puras, mai lura da hakkokin kiwon lafiya.
Sai kuma Mr. Olivier De Schutter, wakili na musamman mai lura da hakkokin da suka shafi talauci da kuma hakkokin bil Adama.
Gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudi na naira biliyan 37 domin gyara ginin majalisar dokokin tarayyar kasar zuwa naira biliyan 27.7
Gwamnatin Najeriya yayin gabatar da tsarin kwas kwarimar da tayi wa kasafin kudin kasar na bana a ranar Talata, ta yanke naira biliyan 9.3 daga kasafin kudin gyara ginin majalisun tarayya.
Tun a bara, naira biliyan 37 da aka sanya cikin kasafin kudin Najeriya na bana domin gyara ginin majalisun dokokin tarayya, ya janyo cece-kuce gami da suka daga bangarori da dama a fadin kasar.
Galibin 'yan Najeriya suna cewa wannan ba komai bane illa barnar kudi da al mundahana, sannan kwata-kwata ba ya kan tsarin lura da halin da ake ciki.
Sai dai a yanzu 'dole kanwar naki' ta jefa gwamnatin cikin dogon nazari tare da yin bita a kan kasafin kudin kasar na bana da shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu tun a bara.
Biyo bayan karyewar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da kuma hasashen raguwar kudaden shiga da gwamnati za ta samu, ya sanya ta zaftare wani kaso daga kasafin da ta kiyasta

No comments:
Post a Comment