Tattalin arzikin Najeriya zai yi mummunan tabarbarewa – Bankin Duniya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Friday, June 26, 2020

Tattalin arzikin Najeriya zai yi mummunan tabarbarewa – Bankin Duniya

Tattalin arzikin Najeriya zai yi mummunan tabarbarewa – Bankin Duniya

Tattalin arzikin Najeriya ya na fuskantar barazanar da ba a taba gani ba, tun a 1985

- Annobar Coronavirus ta karya darajar danyen mai tare da jefa Najeriya a matsala.

- Bankin Duniya ya ce a karshen 2020 za a samu karin Talakawa mutune miliyan 7 a Najeriya.

Bankin Duniya ya ce annobar cutar COVID-19 da kuma karyewar farashin mai a kasuwar Duniya ya janwo tattalin arzikin Najeriya zai shiga cikin matsalar da aka dade ba a ga irinta ba.

Nazarin da bankin Duniya yayi ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai shiga irin halin da ya samu kansa a tsakiyar shekarun 1980 Wanda a wancan lokaci soji ne suke rike da mulki a kasar.

A wani jawabi da babban bankin ya fitar mai taken: “Najeriya a lokacin annobar COVID-19: Shirya tubulin babbako da tattalin arziki’, an yi hasashen tattalin Najeriya zai tsuke da – 3.2% a 2020.

IMF bankin bada lamuni na Duniya yana ganin tattalin kasar zai motsa ne da maki – 5.4% saboda annobar COVID-19.

 An yi wannan hasashe ne, a kan kasar za ta ci karfin COVID-19 a karshen bana.

Kamar yadda Hukumar da kuma bankin Duniya suka nuna, Najeriya tana samun fiye da 80% na kudin kasar waje ne daga arzikin mai, wanda shi ne 50% na kudin shigan da kasar take samu.

Rahoton ya ce: “Saukar farashin mai a kasuwa, ana sa rai a samu raguwar kudin shiga a asusun gwamnati, bayan saukar da karfin GDP zai yi daga 8% zuwa 5% a 2020.”

“Najeriya tana bukatar tsare-tsare da manufofin tattali da za su zaburar da arzikin kasar.”

Barazanar da kasar za ta shiga zai zarce matsalar kudi kawai, COVID-19 za ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da-dama, kuma annobar za ta jefa mutane miliyan bakwai ko fiye da haka cikin talauci.

Rahoton bankin Duniyan ya ce: “A yayin da ada, ake tunanin cewa talakawa za su karu da miliyan biyu, saboda karin adadin jama’a,  to ayanzu alkaluman za su tashi ne zuwa mutum miliyan bakwai.”

"Kason marasa hali zai tashi daga 40.1% da aka samu a 2019 zuwa 42.5% a shekarar nan."

No comments:

Post a Comment