Yayinda sabbin mutanen ke Kara kamuwa da cutar Korona a Najeriya, kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa PTF ya ce lokaci ya yi da za'a mayar da dokar hana fita.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana yiwuwar sake sanya dokar, jiya yayin hirar kwamitin da manema labarai a Abuja
Ya nuna bacin ransa yadda yan Najeriya ke yiwa cutar rikon sakainar kashi.
Yace: "Shin kun san gaskiyar magana? Da ina da iko, lokacin mayar da dokar kulle yayi.
Dokar hana fitar ba abu bane mai dadi, amma lokacin mayarwa yayi saboda yadda naga mutane na yiwa abin rikon sakainar kashi."
Yayinda yake kira ga yan Najeriya su dau abin da gaske, Boss Mustapha ya ce mutane su mayar da hankali wajen bin shawar wari da ka'idojin hukumar.
"Na ga yadda ake wasa da COVID-19 a yau. Mutane na yi kamar cutar ta wuce. Wannan ba abin wasa bane kuma ina kira ga yan Najeriya masu sauraron mu cewa; mu dau abin nan da gaske."
"Kawo yanzu da mutane 549 sun mutu, ba zaka jahilci abin ba, ba zai yiwu kace baka san ko mutum daya da ya kamu da cutar ba." Yace
Ya ce sun gano har yanzu mutane da dama basu yarda akwai cutar ba shi yasa ake kin bin dokoki.
No comments:
Post a Comment