An fasa rubuta rubuta jarabawar WAEC a Najeriya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Wednesday, July 8, 2020

An fasa rubuta rubuta jarabawar WAEC a Najeriya

Ba Za a Gudanar Da Jarabawar WAEC Ba a Wannan Shekarar

Gwamnatin Najeriya ta soke matakin bude makarantu ga daliban da zasu rubuta jarabawar WAEC a wannan shekarar.

Ministan harkokin ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da yayi da manema labarai da yammacin yau.

Adamu ya ce makarantu ba zasu bude ba har sai an tabbatar da cewa Covid-19 ba za ta iya yi wa dalibai illa ba.

Ya kara da cewa, babu makarantar da za ta yi WAEC a Najeriya a wannan shekarar.

Hakan na zuwa ne bayan da Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana a ranar Talata cewa za a gudanar da WAEC a cikin watannin Augusta da Satumba

Majalisar dattawa ta mayar da wa'adin babban sufeton Æ´an sanda shekara https://www.arewagist.com.ng/2020/07/majalisar-dattawa-ta-mayar-da-waadin.html?m=1

No comments:

Post a Comment