Majalisar dattawan Najeriya ta sauya dokar wanda ya cancanci ya rike muƙamin shugaban sufeton ƴan sandan ƙasar zuwa shekara hudu.
Majalisar ta sauya dokar ne bayan ta yi nazari kan tsohuwar dokar ƴan sanda ta 2004 sannan ta sauya ta zuwa ta 2020.
Da yake gabatar da rahoto kan ƙudurin shugaban kwamitin da ake lura da harkokin 'yan sanda na majalisar Halliru Jika cewa ya yi, mafi yawan masu ruwa da tsaki ba su goyi bayan yadda majalisar ke tabbatar da sufetocin 'yan sanda ya yin wani sauraren ra'ayi.
"An samu rabuwar kawuna kan wannan doka da ta buƙaci tabbatar da nadin ko cire babban sufeton 'yan sanda da majalisa ke yi," in ji Halliru.
Dangane da naɗi ko kuma sake naɗa sefetocin 'yan sanda a kasar majalisar za ta ci gaba da bin doron dokar da ake da shi a kasa na 215 da aka yi bayani a kundin tsarin mulki.
No comments:
Post a Comment