Ƴan sanda sun yi Ram da matar da kashe Mijinta - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, July 12, 2020

Ƴan sanda sun yi Ram da matar da kashe Mijinta

Rundunar 'Yan sanda a jihar Abia ta kama wata Mrs Rose Uwaga a kan zargin sheke mijinta mai shekara 83, Alhaji Isa Uwaga a Umuahia babban birnin jihar.

Kakakin rundunar ta jihar, Geoffrey Ogbonnaya ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai, na ƙasa NAN, kama matar mai shekaru 73 a garin Umuahia a ranar Laraba.

Ogbonnaya ya ce daya daga cikin yayan Uwaga, Ibeabuchi, ne ya kai wa 'yan sanda rahoto a kan lamarin a ranar 2 ga watan Yuli.

Ya ce an mika binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka na 'yan sandan wato CID domin zurfafa bincike.

Ya kuma ce gawar mamacin tana dakin ajiye gawa na asibiti "inda ake sa ran gudanar da bincike a kan ta don sanin anihin abinda ya kashe mutumin."

NAN ta gano cewar ma'auratan sun samu rashin jituwa har ta kai ga dambacewa a gidan su da ke Ohobo-Afara Umuahia.

"Yayin fadan, mutumin ya ɗakko adda domin ya firgita matar amma ta fi karfinsa ta murde hannunsa.

"Addar ta fadi daga hannunsa kuma matar da ke da girman jiki ta danne shi a kasa ta shake masa wuya har sai da ya mutu," a cewar wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa.

Muddin muna tare da miji na, ba zan taɓa yin arziki a duniya ba - Matar aure ta garzaya kotu

No comments:

Post a Comment