Kafila Ogunsina, mahaifiyar ƴaƴa huɗu a ranar Alhamis to roki wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ile-tunrun Ibadan, ta raba aurenta da saboda mijinta "ƴa daƙile mata arziki a rayuwa".
Kafilat wacce ke ɗinki ta shaidawa kotu cewa tun bayan da ta auri Rafiu shekaru 12 da suka gabata duk wani hanyar arziki ya toshe mata.
"Tunda na shigo gidansa a matsayin matarsa, komai ya tsaya min cak. Ba na gaba, bana baya. Gashi sai dukan ta yake kamar baiwa.
"Rafiu ya kuma lalata duk abinda na mallaka yayin da na shigo gidansa," a cewar Kafilat.
Da yake mayar da ba'asi a kotun, Rafiu ya roki kotu kada ta raba aurensa da matarsa amma bai musanta zargin da ta yi akansa ba.
An fara ɗaukar Aikin ɗan Sanda ga Abubuwa 14 da ya kamata ka sani kafin Neman aikin
Rafiu, mai sana'ar aikin gini, ya nemi kotu ta taya shi rokon alfarma wurin matarsa kada ta rabu da shi.
"Mai girma mai Shari'a, kada ka raba mu. Ita ce rayuwa ta, gashi kuma ta iya kula da gida sosai.
"Babu tabbas zan iya sake samun wata mace kamar ta," a cewar Rafiu.
Shugaban Kotun, Cif Henry Agbaje ya roki wacce ta shigar da ƙarar ta ƙara haƙuri da mijinta.
Agbaje ya umurci ma'auratan biyu su taho da ƴan uwansu kotu a zaman da za a sake yi.
Ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Agustan 2020 don yanke hukunci.
No comments:
Post a Comment