Cacar baki ta ɓarke tsakanin manyan 'yan siyasa biyu game da zaɓen gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Wani bidiyo na yawo a shafukan sada zumunta inda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda shi ne jagoran kamfe na PDP a zaben gwamna a jihar Edo yana zolayar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje cewar 'dala' ba za ta yi tasiri ba a zaben.
Kalaman na Wike sun kasance martani ga shugaban yaƙin neman zaɓe na APC, wato Gwamna Ganduje wanda bayanai suka ambato shi yana cewa kafin zaɓen gwamnan jihar Edo, 'za mu kai Wike wurin killace masu cutar korona'.
An hana waƙoƙin yabon Annabi S.AW. a kano sai da izinin gwamnati
A shekarar 2018 aka wallafa wasu bidiyon gwamna Ganduje yana 'zuba daloli a cikin aljihu' wanda ake zargin cin hanci ne daga wani ɗan kwangila a jihar. Ko da yake mukarraban Ganduje sun ce bidiyon ba sahihi ba ne.
Gwamna Wike, a jawabinsa wajen Ƙaddamar da kwamitin kamfe na PDP a Abuja, ya ce 'babu wanda zai buɗe mana ido kan zaɓen jihar Edo'.
"Na karanta a jaridu cewa Gwamna Ganduje ya ce za a kai ni wajen killace masu fama da cutar korona har sai an kammala zaɓen Edo, shin wa ya kamata a kai cibiyar?," in ji Wike.
Gwamna Wike ya ƙara da cewa abin da bai sani ba shi ne cewa "mu mutanen Neja Delta za mu karɓi dala sannan mu juya masa baya. Ganduje dalarka ba za ta yi aiki ba a Edo".
Matuƙar Zarge-Zargen da ake wa Magu suka tabbata, to babu wata Nasara da Gwamnati ta samu -cewar Masana
Batun zaɓen gwamnan jihar Edo na ci gaba da jan hankali sosai a Najeriya musamman tsakanin 'ya'yan manyan jam'iyyun siyasar ƙasar watau APC da PDP inda kowacce ke kokarin ganin ita ce ta yi nasara.
A ranar 19 ga watan Satumba ne za a yi zaɓen tsakanin gwamna Godwin Obaseki na PDP da kuma Fasto Ize Iyamu na PDP.
No comments:
Post a Comment