Ofishin mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya musanta cewa ya karɓi naira biliyan hudu daga hannun Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC da gwamnatin Najeriya ta dakatar domin biyan wata buƙata ta ƙashin kansa.
Wata sanarwa da Laolu Akande wanda shi ne kakakin mataimakin shugaban ƙasar ya fitar ta ƙaryata wasu labarai da aka wallafa a wasu jaridu na intanet da wasu saƙonnin Twitter da aka wallafa kan batun.
Labaran da aka wallafa a wasu jaridu biyu na tuhumar Ibrahim Magu da yin sama da faɗi da kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan 39, kuma wai Magun ya ba Mista Osinbajo naira biliyan huɗu cikin kuɗin.
Binciken Magu: Osinbajo ya rubuta takardar korafi zuwa ofishin IGP
Wata tuhumar ta daban kuma na cewa wai mataimakin shugaban na Najeriya ya umarci shugaban na EFCC ya saki wasu ƙaddarorin da hukumar ta kama ba tare da an bi matakai na shari'a ba.
Kakakin mataimakin na Najeriya ya kuma ƙaryata dukkan labaran da ke yawo kan wannan batun, kuma ya bayyana su a matsayin wani yunƙuri na ɓata sunan mataimakin shugaban Najeriya a idon duniya.
Ya kuma ce mataimakin shugaban kasar ba zai bari wannan yunƙurin ya kawar da shi daga aikin gina kasa da yake yi ba.
A karshe sanarwar ta ce Mista Osinbajo ya miƙa wannan batun ga hukumomin tsaron kasar domin su gudanar da bincike da zumar hukunta waɗanda suka wallafa labaran.
Shi dai Ibrahim Magu ya shafe kusan shekara biyar yana jagorantar hukumar EFCC, amma a halin yanzu yana fuskantar bincike daga wani kwamitin da shugaban kasa ya nada kan wasu tuhume-tuhume da ake masa na aikata laifukan cin hanci da rashawa da rashin yin biyayya ga magabatansa.
No comments:
Post a Comment