ISIS da Al-Qaeda 'sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya
Gwamnatin kasar Amurka ta bayyanawa duniya cewa mambobin ƙungiyar ƴan ta'addan Al-Qa'ida sun fara ratsawa jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.
Kwamandan Sojin Amurka na harkoki na musamman a nahiyar Afrika, Dagvin Anderson, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ya ce kungiyar na shiga wurare daban-daban a yammacin Afrika.
A jawabin da TheCable ta samu daga ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Anderson ya ce Amurka za ta cigaba da hada kai da Najeriya wajen raba bayanan binciken sirri.
Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sune: Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Kebbi, da Sokoto.
Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro umarnin sabunta dabarun yaƙar ta'addanci
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/buhari-ya-baiwa-hafsoshin-tsaro-umarnin.html
"Muna hada kai da Najeriya kuma zamu cigaba da hadawa wajen raba bayanan sirri da wajen fahimtar abubuwan da wadannan yan ta'addan ke yi."
Kuma hakan ya taimaka musu wajen ayyukansu a jihar Borno da kuma Arewa maso yammacin Najeriya da muka ga yan Al-Qa'ida sun fara shiga."
"Amma matsayinmu na al'ummar kasashen duniya, mu kan yi tunanin mun kawar da su ne kuma suna gab da wargajewa."
"Ina tunanin bayan shekaru 20 mun gano cewa suna da taurin kai, duk da kanana ne, suna amfani da kafafen sada zumunta wajen ɗaukan sabbin mambobi kuma suna samu." Yace
Anderson ya ce abinda zai sa kokarin kasashen duniya ya haifi ɗa mai ido shine idan gwamnatin Najeriya da kanta tayi hoɓɓasa wajen gudanar da yaƙi.
"Idan aka zo lamarin Najeriya kuwa, Najeriya na da muhimmanci ga yankin Afrika ta yamma."
"Saboda haka babu kasar da za ta magancewa Najeriya matsalarta. Zamu iya taimakawa, Birtaniya da sauran kasashe zasu iya taimakawa, amma wajibi ne Najeriya ta tashi tsaye domin mu san da gaske take." Yace
Ana fuskantar hare-hare a jihohin Arewa maso yamma musamman Katsina, Sokoto da Zamfara.
GWAMNA ZULUM YA TONA ASIRIN WAƊANDA SUKE CIN AMANA A YAƙI DA TA'ADDANCIN BOKO HARAM
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/gwamna-zulum-ya-tona-asirin-waanda-suke.html
A baya Legit Hausa ta rawaito cewa Rahotanni na yawo cewa wasu ɗinbin ɗan ta’addan kungiyar Boko Haram na ɓangaren Abubakar Shekau, sun fitar da sabon bidiyo na musamman.
‘Yan ta’addan da sukayi wa Abubakar Shekau mubaya'a sun ce sun dauki wannan bidiyo ne a jihar Neja da ke a yankin Arewa maso tsakiyar kasar.
Malam Audu Bulama Bukarti, wani masanin harkar tsaro ya bayyana wannan a shafinsa na Twitter. A wannan bidiyo an ga mutane kimanin dari suna gabatar da sallar idi a ƙungurmin daji.
Daga baya wasu sojoji uku suka yi jawabin barka da sallah. Wadannan mayaka sun yi magana ne da harshen Hausa, Ingilishi da kuma Fulfulde.
Mutane 135 sun mutu 5,000 suka jikkata Sakamakon fashewar wasu sinadarai a Lebanon https://www.arewagist.com.ng/2020/08/mutane-135-sun-mutu-yayin-da-mutane.html
Mutane 135 sun mutu 5,000 suka jikkata Sakamakon fashewar wasu sinadarai a Lebanon https://www.arewagist.com.ng/2020/08/mutane-135-sun-mutu-yayin-da-mutane.html
No comments:
Post a Comment