Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, ya yi watsi da rahotan Jaridar Sahara Reporters da tayi ikirarin cewa ya sayi sabbin gidaje uku ya ajiye iyalinsa a Abuja.
Ministan ya yi martanin ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, da yammacin Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.
Ta ce ya kamata a sani cewa kudin albashin da Malam Pantami ke samu a yanzu a matsayin minista bai kai kudin da yake samu lokacin da yake karantarwa a jami'ar Madina ba.
Haka zalika ba duniya ke gabbansa ba kawai ya dawo Najeriya ne domin taimakawa cigaban kasa.
Jawabin yace: "Dr Isa Pantami na daya daga cikin yan tsiraru a Najeriya da duniya bata damesu ba, kawai kishin kasa da sadukar da kai ya sanya ya amsa kira dawowa gida.
Kawai dan fayyace gaskiya, Ministan bai sayi gida ko daya ba a duniya tun lokacin da ya hau Minista ba."
"Daya daga cikin gidajen da aka wallafa wanda ministan ya ke zama ne tun Junairun 2017, sama da shekaru biyu kafin zama minista.
Dayan gidan kuma haya ya karba tun daga ranar 17 ga Disamban 2019."
Jaridar Sahara Reporters ta wallafa hotunan wasu manya gidaje da ta ikirarin cewa Ministan Sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya ajiye matansa uku a Abuja.
Jaridar ta ce Ministan na shagalinsa a Abuja.
No comments:
Post a Comment