Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa da ke cewa an sanya dokar hana tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen biyu.
Cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke birnin tarayyar Abuja ya fitar ta ce, babu wani mataki da aka ɗauka tun bayan na taƙaita tafiye-tafiye da aka yi ga ko wacce ƙasa saboda annobar korona a ranar 7 ga wata Maris, a wani mataki na daƙile annobar korona a kasar.
Bayan samun sauƙi da aka yi na wannan annoba, sai aka janye haramcin tafiye-tafiyen da aka sanya a ranar 7 ga wata Yuni ga duk wani mai zuwa ziyara kasar, tare da umarnin cika sharuddan da aka gindaya.
Kuma dukkan sharudan da aka sanya babu wanda aka ware Najeriya cikinsu.
Sanarwar ta ce a yanzu da ba a yin tafiya, hakan na da alaka da rashin saukar jiragen kasashen duniya a Najeriya, ma'ana Najeriya ba ta buÉ—e filayane jiragenta ba.
UAE na ta kokarin tattaunawa da Najeriya domin ganin an dawo da yin tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu.
Ofishin jakadancin da ya wallafa sanarwar a shafinsa na Twitter, ya shawarci mutane da su rika tuntubar hukumomi domin samun labarai masu inganci
ISIS da Al-Qaeda 'sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya
No comments:
Post a Comment