Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da ke kudancin Najeriya ya cire duka rufin majalisar dokokin jihar da zummar hana kowa zama cikin ginin majalisar.
Wannan na zuwa ne bayan da ‘yan sanda suka yi wa ginin majalisar jihar ƙawanya wadda ke Benin babban birni jihar.
Kakakin gwamnan Obaseki ya shaida wa BBC cewa ya yi hakan ne da nufin hana wasu 'yan siyasa ciki har da gwamnan wata jiha cika burinsu na kwace jihar lokacin da ake daf da gudanar da zaben gwamna a jihar.
Gwamman jami’an tsaro ne suka sanya shinge a wajen ginin majalisar.
Kakakin ‘yan sandan jihar Chidi Nwabuzor ya bayyana cewa jami’an sun je ne da nufin kare rikicin da ake zaton zai iya tashi.
Rikicin siyasa na ƙara ƙamari a jihar da aka tsara yin zaɓen gwamna a watan Satumbar gobe.
Rahotanni sun ce babu dai kowa a cikin ginin majalisar. Kimanin mutum 200 ne suka yi carko-carko a wajen ginin majalisar, kuma mafi yawansu magoya bayan gwamna mai ci ne.
Al’amura na kara rikicewa tun bayan tuɓe mataimakin kakakin majalisar Yekini Idaiye da aka yi a ranar Laraba kan zargin shi da karya doka.
A baya ya fito ƙarara ya nuna goyon bayansa ga abokin hamayyar gwamna mai ci.
A sauya sheƙar da yayi na ban mamaki a watan Yuni, Gwamna Godwin Obaseki, ya sauya daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP
ISIS da Al-Qaeda 'sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya
No comments:
Post a Comment