Gwamnatin Burtaniya ta Hana mutanan ta zuwa wasu jihohin Najeriya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, August 8, 2020

Gwamnatin Burtaniya ta Hana mutanan ta zuwa wasu jihohin Najeriya

A hana Turawan Birtaniya tafiya arewacin Najeriya


Gwamnatin Birtaniya ta shawarci al’ummarta da ke zaune a Najeriya da su Æ™aurace wa tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin arewaci da kudancin kasar saboda taÉ“arÉ“arewar matsalar tsaro.


Jihohin sun hada da Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da Kano da Bauchi da Niger da Jigawa da Katsina da Zamfara da Kogi da Abia da kuma Rivers.


Sauran jihohin sun hada da Delta da Bayelsa da Akwa Ibom da kuma Cross River.


Sanarwar da Birtaniya ta fitar a shafin ofishinta mai kula da lamurran kasashen Æ™etare ta ce, matsalar tsaro ce ta tilasta É—aukar matakin wucin gadi na janye wani adadi na ma’aikatanta da ke Ofishin Jakadancinta na Abuja da kuma karamin Ofishin Jakadancinta da ke birnin Lagos.


Kodayake ofisoshin biyu na ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka da suka hada da taimaka wa Turawan Birtaniya da ke zaune a Najeriya.


A bangare guda, Birtaniyar ta ce, kungiyoyin Æ´an ta’adda masu nasaba da Al Qaeda na gudanar da aikinsu a jihar Kaduna kamar yadda ta samu rahotanni a cewarta.


Jihohin arewacin Najeriya musamman Borno da Yobe na fama da rikicin Boko Haram, yayin da 'yan bindiga suka addabi Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.


No comments:

Post a Comment