Gwamnatin Kano ta bayyana wasu wurare 12 da ta ware don daliban dake ajin karshe na babban sakandare su rubuta jarabawa.
Babban Sakataren hukumar kula da makarantun gwamnati Bello Shehu ya sanar da haka da yake ganawa da manema Labarai a Kano.
Ga yadda tsarin yake:
1 – GGUC Kachako, GGSS Sumaila da GGSS Albasu zasu rubuta jarabawa a makarantar gwamnati na Mata dake Kachako , wato Government Girls Unity College, Kachako.
2 – GGSS Kura da GGSS Madobi za su rubuta jarabawa a makaranta sakandaren Mata na gwamnati dake Kano, wato GSS Government Girls College, Kano
3 – GGASS Danbatta da GGASS Tudun Wada za su rubuta jarabawa a Government Girls Arabic College Goron Dutse.
4 – GGSS Kwa za su rubuta jarabawa a Government Girls College Dala.
5 – GSS Yar Gaya and GGSS Kabo za su rubuta jarabawa a Government Girls Secondary School Shekara
6 – GGC Gezawa da GGSS Jambaki za su rubuta jarabawa a Government Girls Secondary School Jogana.
7 – GSS Kafin Mai-Yaki, GC Tudun Wada da GSS Kwankwaso za su rubuta jarabawa a Government Secondary School Karaye
8 – GSS Rano, GASS Tsangaya da GSS Ajingi za su rubuta jarabawa a Government Secondary School Sumaila
9 – GSS Bichi, GSS Bagwai da GSCS Wudil za su rubuta jarabawa a GSS Danbatta
10 – GSS Dawakin Tofa za su rubuta jarabawa a Government Secondary School Gwarzo
A karshe Shehu ya ce dalibai a wasu makarantu 161 za su rubuta jarabawar su a makarantun su ne.
Dalibai sama da 11,000 ne zasu rubuta jarabawar karshe a jihar Kano wanda za a fara a cikin Agusta.
No comments:
Post a Comment