Ƙasashen Musulmi sun fara ƙaurace wa kayan Faransa - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, October 26, 2020

Ƙasashen Musulmi sun fara ƙaurace wa kayan Faransa

 


  Ƙasashen Musulmi sun fara ƙaurace wa kayan Faransa 

Tuni an fara cire kayan da Faransa ke samarwa a wasu shaguna da ke Kuwait da Jordan da kuma Qatar


Faransa ta bukaci kasashen Gabas Ta Tsakiya da kada su amince da kiraye-kirayen ƙaurace wa sayen kayayyakinta.


Kauracewa kayayyakin da Faransa ke sayarwa wani ɓanagare na nuna fushi kan matakin Shugaba Emmanuel Macron na kare zanen fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).


Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce kiran da wasu masu tsattsauran ra'ayi ke yi na ƙaurace wa kayanta 'ba shi da tushe'.


Tuni an fara cire kayan da Faransa ke samarwa a wasu shaguna da ke Kuwait da Jordan da kuma Qatar.


Haka ma an gudanar da zanga-zanga a Libiya da Syria da kuma Zirin Gaza.


Duk kuma hakan na faruwa ne tun bayan kalaman Macron kan kisan gillar da aka yi wa wani malamin makaranta da ya nuna wa ɗalibansa zanen Annabi Muhammad (SAW).


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296


Me  Emmanuel Macron ya ce kan addinin Musulunci?

An ambato Macron yana cewa "an kashe Samuel Paty ne saboda masu tsattsauran ra'ayin Islama na son ƙwace gobenmu, to amma Faransa ba za ta taɓa ba da gari ba kan zanen barkwancin."


Bugu da ƙari, Macron ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa "Ba za mu taɓa ba da kai ba."


Nuna hoto ko zanen Annabi Muhammad (SAW) babban laifi ne a koyarwar addinin Musulunci.


To amma Faransa na kallon kanta a matsayin ƙasar da al'umma ke da ƴancin faɗar albarkacin bakinsu kan abubuwa da dama.


Kasashen Musulmi na duniya da suka hada da Yammacin Turai na zargin Macron da ƙoƙarin takura wa Musulmi ta hanyar halasta ƙyamar addinin Musulunci


Martanin kasashen Musulmi

Shugabannin siyasa a Turkiyya da Pakistan sun zargi Macron da rashin girmama ƴancin addini da kuma shiga hakkin Musulmi a Faransa.


Ko a ranar Lahadi shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shawarci Mr Macron da yaje ayi masa gwajin kwakwalwa kan yadda yake kallon addinin musulunci.


Hakan ya fusata Faransa, wanda yasa ta janye jakadanta da ke Santambul.


Shi ma shugaban Pakistan Imran Khan ya zargi Macron da faɗa da addinin Musulunci kuma ya nuna ƙarara cewa ya jahilci wane irin addini ne.


Batun ƙaurace wa kayan Faransa shi ne maudu'i na biyu da yafi jan hankali a Saudiyya, ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a Gabas Ta Tsakiya.


Dama tun kafin kisan Samuel Paty Macron ya sanar da tsauraran dokoki kan abin da ya kira "shirin masu tsattsauran ra'ayi kan Faransa."


Matakin ya ƙara sa Musulmin Faransa fargabar cewa gwamnati na yunƙurin yi musu katsalandan ga addini.


Haka ma Macron ya kuma ce Musulmin Faransa su miliyan shida na cikin haɗari yayin da addininsu ke 'cikin rikici'.


Zanen Annabi Muhammad (SAW) ya kawo sauyi a siyasar Faransa.


Ko a shekarar 2015 an kashe mutum 12 a hari kan ofishin mujallar barkwanci Charlie Hebdo, wadda ta wallafa zanen a shafukanta.


Ba a Gabas Ta Tsakiya kaɗai ba, ko a sauran ƙasashen Musulmi na duniya da suka haɗa da Yammacin Turai ana sukar Mr Macron da ƙoƙarin takura wa Musulmi ta hanyar halasta ƙyamar addinin.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

1 comment:

  1. I Abubakar Sabo Dauda by name, from Taraba State, you are programs is very nice,ispecily how to sale date in good way.thanks for giving me opportunity to comment on you.

    ReplyDelete